Jami’an tsaro sun garƙame inda su Malam Shekarau da jama’arsu za su gudanar da zaɓe

1142

Tsagin APC da ke adawa da salon shugabancin jam’iyyar a Jihar Kano bai samu damar gudanar da zaɓen shugabancin jam’iyyar ba yayin da ɓangaren gwamnati ke aiwatar da nasa.

Tun da farko wadannan jiga – jigai na jam’iyyar APC ƙarƙashin jagorancin Malam Ibrahim Shekarau sun shirya yin zaɓen jam’iyyar ne a makarantar koyon sana’a ta Sani Abacha Youth Centre da ke kan titin Madobi a jihar Kano, inda ake sa ran za su zaɓi Alhaji Ahmadu Haruna Zago a matsayin shugaban jam’iyyar.

Wani ɓangare na mahalarta taron zaɓen shugabancin jam’iyyar APC tsagin Malam Shekarau

Sai dai jami’an ƴan sanda sun hana kowa shiga wurin taron da aka niyyar gudanarwa a yau Asabar.

Jagororin taron sun bayyana cewa za su sanar da wata ranar da za su gudanar da zaɓen.

Wannan dai yana zuwa a daidai lokacin da ɓangaren gwamna Abdullahi Umar Ganduje wanda su ke fatan ganin Abdullahi Abbas Sanusi ya zama shugaban jam’iyyar tuni aka fara kada kuri’a.

Jam’iyyar APC na gudanar da taruka a faɗin Najeriya da zummar zaɓen shugabanninta a kowane mataki yau Asabar.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan