Kwankwaso Ya Guje Wa Kamu, Ya Miƙa Kansa Ga EFCC

436

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Kwankwaso, ya miƙa kansa ga Hukumar Hukunta Masu Yi Wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Zagon Ƙasa, EFCC, a cewar wani rahoto na jaridar Intanet, Premium Times.

Wannan dai ya zo ne makonni bayan jaridar ta kawo rahoton yadda jigajjigan jam’iyyar hamayya ta PDP suke kauce wa gayyatar EFCC.

Kai kan nasa ba zai rasa nasaba da guje wa kamu ba daga hukumar, kamun da Premium Times ta ce EFCC na shirin yi.

Manyan jami’an EFCC da suka nemi a ɓoye sunansu saboda ba a ba su iznin yin magana ba sun faɗa wa Premium Times cewa Kwankwaso ya kai kansa hedikwatar EFCC ne ranar Asabar da rana.

“Wannan ya zo ne bayan gayyata daban-daban da bai amsa ba”, in ji ɗaya daga cikin jami’an.

Ba a iya samun Wilson Uwujaren, Jami’in Huɗɗa da Jama’a na EFCC ba.

Wani hadimin Kwankwaso na kusa ya ce zai yi wa Premium Times ƙarin bayani, amma har lokacin haɗa wannan rahoto bai ce komai ba.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan