Mun Fitar Da ‘Yan Najeriya Miliyan 4 Daga Talauci— Ministan Noma

480

Ministan Noma da Raya Karkara na Najeriya, Mohammed Abubakar, ya ce an fitar da ‘yan Najeriya miliyan 4.2 daga talauci ta fannin aikin noma a cikin shekara biyu da suka gabata.

Ministan ya bayyana haka ne ranar Juma’a a Abuja a yayin taron Ranar Abinci ta Duniya.

“A matsayin wani ɓangare na yunƙurimmu don tabbatar da wadatuwar abinci, an samar da wuraren samar da ruwa har 446 a ƙauyuka, inda iyalai 286,500 suke amfana.

“Mun kuma samar da kayayyakin lantarki har11,952, samar da tiransifoma mai ƙarfin 500KVA don sauƙaƙa sarrafa abinci ta hanyar amfani da wutar lantarki.

“Bugu da ƙari, ta hanyar shirye-shiryenmu daban-daban, mun fitar da ‘yan Najeriya miliyan 4,205,576 daga talauci a cikin shekara biyu da suka gabata.

“Wannan zai ci gaba a matsayin wani ɓangare na alƙawarin Shugaban Ƙasa na fitar da ‘yan Najeriya miliyan 100 daga talauci a shekaru 10 masu zuwa”, in ji shi.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan