Ranar abinci ta duniya: Ya farashin kayan abinci ya ke a inda ku ke?

475

Majalissar Dinkin Duniya ta ware ranar 16 ga watan Oktobar kowacce shekara, domin tunawa da muhimmancin abinci ga rayuwar dan Adam a duniya.

Abinci dai shi ne ginshikin rayuwa, kuma muhimancin abincin ga rayuwar dan Adam ya sa Majalissar Dinkin Duniyar ta ware wannan rana.

Sai dai bikin na wannan shekarar ya zo a daidai lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ke gargadi na gagarumar matsalar karancin abinci da fargabar hauhawr farashin kayan abinci a faɗin duniya.

Wasu Iyalai suna cin abinci

Harkar noma da samar da abinci na daya daga cikin bangarorin dake samun koma baya a kasashe masu tasowa, abinda ya sa kasashe da dama basa iya noma abinda zasu ciyar da al’ummar su.

Noma domin ciyar da al’umma na daya daga cikin manyan sana’oin da jama’ar wannan sashe na duniya suka dogara da shi, kafin matsalolin yau da kullum suka tilastawa wasu mutane watsi da harkar domin rungumar wasu sana’oin da suke ganin zasu fi taimaka musu.

Cigaban zamani ya kuma inganta yadda ake noman wajen samar da na’urori da ake amfani da su da kuma iri da takin zamanin dake bada damar noma manyan gonaki, sabanin yadda aka saba gani a shekarun baya.

Talauci da rashin samun tallafi na hana manoma marasa karfi samun irin wadannan na’urori domin inganta noman da suke, abinda ya sa ayau wasu daga cikin su basa iya noma abinda zasu ci na shekara.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan