Abdullahi Umar Ganduje ya zama Gwarzon gwamna na shekarar 2020

462

Kamfanin Jaridar The Sun ya karrama gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje da lambar yabo ta gwarzon gwamna na shekarar 2020.

Taron karramawar ya gudana a daren jiya Asabar a otal ɗin Eko da ke birnin Lagos ya samu halarcin manyan jami’an gwamnatin Kano da fitattun ƴan siyasa daga jihar Kano.

Lokacin da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ke karɓar lambar yabon

Tun da farko mai taimakawa gwamna na musamman akan harkokin shafukan sadarwa na zamani, Abubakar Aminu Ibrahim ya wallafa labarin tare da hotunan a shafinsa na facebook.

A lokacin da ya ke miƙa lambar yabon ga Gwamnan, tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Ambasada Baba Gana Kingibe ya ce gidan jaridar The Sun sun karrama gwamnan ne duba da yadda yake hidimtawa al’ummar sa ta jihar Kano ta hanyoyi daban-daban.

Jaridar ta The Sun ta bayyana cewa la’akari da irin manyan ayyukan raya ƙasa da gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ke yi a jihar Kano, da su ka haɗa gina kasuwar kasuwanci ta Kanawa da ke kan hanyar Zaria da kuma baiwa mata jarin fiye da Naira biliyan huɗu da kuma horar da matasa sana’o’in dogaro da kai da inganta kiwon lafiya na daga cikin abubuwan da ta yi la’akari da su wajen ba shi lambar yabon.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan