Watanni biyu kafin zaɓe zamu tare hanyoyin fita daga Kano – Sanata Rufa’i Hanga

702

Tsohon shugaban rusasshiyar Jam’iyyar CPC na kasa kuma tsohon Sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya a majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Rufai Sani Hanga ya bayyana cewe za su kira gagarumar zanga zanga watanni biyu kafin zaɓen shekarar 2023 domin tabbatar da cewar babu wanda ya gudu daga cikin jihar Kano.

Sanata Rufa’i Hanga ya bayyana hakan ne a cikin wani faifan bidiyo da ya wallafa, inda ya ƙara da cewa kowa sai ya mika mulki da hannunsa kamar yadda ya karba, daga nan ne kuma za su dauki mataki na gaba, wajen ganin an tuhumi duk wadan da ake zargi da almubazzaranci da dukiyar jama’a.

Sanata Rufa’i Sani Hanga

Sanata Rufai Hanga na martani ne akan yadda matar gwamnan jihar Kano ta zama wuƙa da nama akan duk wani al’amari da ya shafi bayar da filaye a Kano.

Haka kuma Sanatan ya zargi matar gwamnan da karɓar kuɗaɗe a wajen mutane domin basu filaye su gina gidajen mai.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan