Yau ta ke Ranar Yaƙi da Talauci: Fiye da ƴan Najeriya Miliyan 7 ne ke fama da talauci

423

Ranar 17 ga watan Oktoba na kowacce shekara rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta ware a matsayin ranar yaki da Talauci a Duniya. An zaɓi ranar ne domin tayar da gwamnatoci, da kungiyoyi daga barci akan maganar samar da hanyoyin fitar da jama’a daga kangin fatara, sakamakon rashin wata kwakkwarar madogara.

Sai dai ranar ta bana na zuwa ne a dai dai lokacin da talaucin ke ƙara yawaita tsakanin al’ummar Duniyar, da masifu irin na yake- yake inda mulkin danniya ne kan gaba wajen hauhawar talaucin.

Haka kuma matsalolin talaucin ya sa yara ƙanana da ba su wuce shekaru goma ba sun fara rungumar sana’oi daban-daban don samun na kalaci a kasashe masu tasowa ciki har da Najeriya.

Hakazalika wata ƙididdiga ta nuna cewa akwai mutane miliyan 700 da su ke fama da talauci a yau, a duniya wadanda da kyar kowannensu ke samun Dalar Amurka 2 a kowacce rana. Bincike na nuni da cewa, kashi 70 daga cikin 100 na waɗannan matalauta na zaune ne a nahiyoyin Afirka, da Asia.

Talauci A Najeriya

Najeriya ta fi kowacce kasa yawan arzikin man fetur da kuma jama’a a Afirka, amma tana sahun gaba-gaba a jerin kasashen da ke fama da rashin ci gaba, abin da ake alakantawa da cin hanci da rashin ingantaccen shugabanci.

Wani sabon Rahoto da Bankin Duniya ya fitar a cikin shekarar nan da mu ke ciki, ya ce tsadar rayuwa da hauhawar farashi na ci gaba da mummunan tasiri a tattalin arzikin Najeriya kuma haka ya tura kara tura ‘yan Najeriya miliyan bakwai cikin halin talauci. Rahoton ya cigaba da cewa kusan kashi 75 bisa dari na al’ummar Najeriya ne suke fama da talauci iri daban-daban kamar fatara, da yunwa, da kuma irin da yau fari gobe baki.

Wasu yara akan bola suna tsince – tsince

Haka kuma rahoton bankin duniyar ya ce in har hukumomi ba su kai ga yin hattara ba musamman ta fannin aiwatar da sauye-sauyen manufofi ma su inganci a harkokin tattalin arziki da hada-hadar kudade, tattalin arzikin kasar nan ka iya samun ci gaba amma cikin yanayi na tafiyar hawainiya. Bankin dai ya nunar, rashin ayyukan yi da yai katutu, yanayi ne da ke dada jefa da daman musamman matasa cikin halin aikata muggan laifuka irin su sace-sace da garkuwa da mutane dan neman kudaden fansa a wasu sassan ƙasar nan.

Wanne Ƙoƙari Hukumomi Su Ke Yi Domin Yaƙi Da Talauci A Najeriya?

A cikin watan Yunin shekarar nan ne shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya kaddamar da wani kwamiti da zai aiwatar da yaki da talauci wanda ake sa ran zai raba yan Najeriya Miliyan 100 daga kangin talauci.

Kwamitin wanda mataimakin shugaban ƙasa Farfesa Yemi Osinbajo zai jagoranta na ƙunshe da manyan jami’an gwamnati da ministoci. Sauran mambobin kwamitin sun haɗa da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, da wasu gwamnonin jihohin ƙasar nan.

Shugaba Muhammadu Buhari

Babbar manufar kwamitin ita ce fitar da mutum miliyan 100 daga cikin ƙangin talauci a cikin shekaru 10.

A ɗaya ɓangaren kuma masana na ganin inganta rayuwar mata ta hanyar ba su jari domin gudanar da kananan sana’oi da kuma mayar da hankali wajen noma, da kiwo na daga cikin hanyoyin da za su taimaka a irin wannan yaki da talauci a Najeriya.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan