Wani kamfanin hada-hadar kayan noma da ke jihar Kano mai suna Silvex International ya ce yana shirin fara zuba jari a wani sabon shirinsa mai laƙabin “shirin rukunin gonaki” a jihohin Jigawa da Nasarawa.
Shirin, a cewar Manajan Daraktan Kamfanin, Abubakar Usman na da nufin cike giɓi a fannin samar da abinci a lokacin da ake fama da matsalar sauyin yanayi.

Abubakar Usman ya bayyana haka ne a Kano a lokacin wani taron da Cibiyar nazarin ayyukan noma ta Jami’ar Bayero wato Centre for Dryland Agriculture, CDA, ta shirya tare da haɗin gwiwar kamfaninsa da wani shirin gwamnatin Birtaniya mai suna LINKS.
“A halin yanzu a Jigawa, muna shirin samun kadada 5,000, tuni an samu 3,000. A Jihar Nasarawa kuma, muna shirin samun kadada 15,000.
“Manufarmu ita ce a samar da iri mai ingancin gaske.
“Mun je ne don samar da wasu manoma a yau, saboda a yau matasa da yawa sun yi amannar cewa noma ba sana’a ba ce mai kawo kuɗi, amma a yanzu muna son canza labarin ta hanyar faɗaɗa hanyoyin noma”, in ji shi.

Abubakar ya ƙara da cewa shirin “rukunin gonakin” yana da nufin sauya al’amura a fannin noma a lokacin da ake fama da sauyin yanayi.
Da yake jawabi tun da farko a taron, Darakta Janar na Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya, NiMET, Dakta Mansur Bako Matazu ya danganta matsalolin ambaliyar ruwa, sauyin yanayi da saukar damina da ƙarewarta ga sauyin yanayi.
Darakta Janar din ya ce a wannan shekara, mafiya yawancin jihohin ƙasar nan ba su samu isasshen ruwan sama ba, abin da ya ce tuni dama NiMET ta yi hasashen haka.
A cewar Daraktan CDA, Farfesa Jibrin Muhammad Jibrin, an shirya taron ne don a yi nazarin batutuwan sauyin yanayi da yadda suke shafar Najeriya da nufin gabatar da su ga mahukunta don ɗaukar mataki.