Fitila: Tankade Da Rairayar Manyar Rahotannin Makon Jiya

596

A wannan Asabar din data gabata ne aka gudanar da zaben shuwagabanni na jahohi na jam’iyar APC wacce ita ce jam’iya mai mulki a wannan kasa. Zaben da aka dade ana dage shi a baya saboda wasu dalilai na ringimun cikin gida an gudanar dashi cikin rudani, inda ka samu wasu jahohin sun gudanar da zaban a bangarorin jagorori daban daban.

Ku duba: Ni Ne Halattaccen Shugaban APC A Kano— Ɗanzago

Tun Kafin dai wannan zabe, jam’iyar APC ta dade a cikin rudani da rigingimu musamman a jahohi irinsu Kano, Ogun da Kwara da kuma jihar Zamfara wadda rigimar cema ta haifarwa da jam’iyar rasa dukkanin mukaman iko a jihar bayan da kotin koli tayi hukuncin cewa jam’iyar bata yi zaben cikin gida yadda ya kamata ba.

Wannan shi ne ya bawa Gwamna Bello Matawalle na jam’iyar PDP a waccan lokaci damar darewa akan kujerar mulki tare da sanatoci, da yan majalisu na tarayya da na jiha na jam’iayyar PDP bayan da kotu ta kori dukkanin wadanda aka zaba a karkashin jam’iyar APC.

Gwamnan Zamfara Bello-Matawalle

Bari muyi duba da matsalolin da jam’iyar ta fuskanta a wannan zabe da akayi sannan kuma muyi duba game da kalubalen da zata fuskanta a zabubbuka masu zuwa musamman a jahohi irinsu Kano, Kwara da Zamfara inda a wadannan jahohi ne rikicin yafi tsamari.

Ana daf da wannan zabe, jaridun kasarnan ciki harda wannan jarida suka rawaito yadda wasu gungun yan majalisar tarayya karkashin jagorancin tsohon gwamnan jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau suka kafa wani sabon tsage a jam’iyar APC a jihar Kano wadda suka yiwa lakabi da G7.

Cikin manyan da aka jiyo sunayensu a waccan tafiya bayan jagoran nasu, sun hada da sanata mai wakiltar Kano ta Arewa wato sanata Barau Ibrahim Jibrin, sai dan majaisa mai wakiltar karamar hukumar birni wato Sha’aban Ibrahim Sharada wanda sun dade suna takun saka da gwamnan, sai dan majalisa wadda ya fito daga mazabar gwamnan wato Abdulkadir Jobe da dan majalisa mai wakiltar kananan hukumonin Gabasawa da Gezawa, Nasiru Auduwa Gabawa.

Wadannan mutane suna zargin gwamna Abdulahi Umar Ganduje tare da shugaban jam’iyar na riko, Abdullahi Abbas da tafiyar da harkokin jam’iyar yadda suka ga dama. Sannan suna zargin cewa ana yin abubuwa da dama batare da an tuntube suba.

Me ya gudana lokacin zabe?

Muyi duba game da zaben daya gudana a ranar Asabar din data gabata, a jihar Kano kamar sauran jahohi irinsu Kwara da Ogun an gudunar da zaben shugabancin jam’iyar ne a bangarori daban daban. Kamar a jihar Kano rahotanni sunyi nuni da cewa zaben anyi shi ne gudu biyu inda aka samu damar fitar da shuwagabanni guda biyu a jam’iyar.

Abdullahi Abbas – Alhaji Haruna Zago

A bangaren tsohon gwamnan wato Malam Ibrahim Shekarau, masu zabe sun samu damar zabar Alhaji Haruna Zago a matsayin shugaban jam’iyar ta APC a jahar kano. Sai kuma a bangaren gwamna inda shugaban jam’iyar na riko, Abdullahi Abbas ya samu damar darewa a kan mukamin shugabanci na jam’iyyar.

To ko shin menene hakan yake haskawa game da zaben game gari a jam’iyar ta APC a 2023?

Zamu yi bayani nan gaba kadan. A jihar Kwara ma dai an samu irin wannan rikici, inda tsagin ministan labarai da al’adu wato Lai Muhammad wanda ake ganin shi ne jagora kuma wanda ya jagoranci kafa mulkin jam’iyar APC a jihar sun gudanar da nasu zaben inda tsagin gwamnan jihar mai ci, Abdurrahman Abdulrazaq suma suka gudanar da nasu zaben.

Tun kafin wannan zabe dai, a can baya an taba jiyo ministan na labarai da al’adu wato Lai Muhammad yana wasu kalamai inda yake cewa ana yin harkokin jam’iya a jihar babu su, sannan yayi ikarin cewa su suka kawo dukkanin wani canji da ake gani yanzu a jihar ta Kwara tare da kwace shugabancin jihar daga hannun gidan Saraki wadanda suka shafe fiye da shekara ashirin suna mulkin jihar. Wannan sabani dai ya jefa jam’iyar a cikin ruduni a jihar kuma masana suna ganin tabbas in shugabanin guda biyu basu dauki mataki ba jam”iyar na iya rasa mulkin jahar.

Sai jihar Zamfara inda tun bayan komawar gwamnan jihar, Bello Matawalle ake samun sabani tsakaninsa da shuwagabannin jam’iyar irinsu tsohon gwamnan jihar wato Abdulaziz Yari da tsohon sanata Kabiru Marafa wadanda a baya basa ga miciji a tsakaninsu wanda hakan ne yasa jam’iyar tayi asarar dukkanin kujeru a jihar, amma jim kadan bayan komarwar gwamnan aka jiyo su suna magana da murya daya.

Tuni dai wadannan mutane suka fitar da sanarwar cewa ba wanda ya isa ya shigo jam’iya daga bayansu ya zama shugabansu. Duk da dai shugaban jam’iyar na kasa na riko, Mai Mala Buni yayi wani zaman sulhu da bagarorin guda biyu a baya, amma masana harkokin siyasa na ganin cewa tabbas wannan rikici na iya jefa jam’iyar tsaka mai wuya a jihar. Bari mu dawo jihar ta Kano muyi duba da irin illar da wannan rikici ka iya kawowa jam’iyar in ba’ayi maganinsa ba.

Mu danyi mi’ara koma baya, a shekarar 2011 lokacin tsohon gwamna mai girma Malam Ibrahim Shekaru yana gwamna an sami wani sabani tsakaninsa da mataimakinsa da wasu kwamishinoni game da wanda ya kamata a fitar a matsayin dan takarar gwamna a waccan lokacin, inda tsagin tsohon gwamnan suka dage akan fitar da kwamishinan kananan hukomin na waccan lokaci wato Salihu Sagir Takai, inda daga wani bangare kuma na jam’iyar suke ganin cewa mataimakin gwamnan wato Abdullahi T. Gwarzo shi ne ya dace ya zama dan takarar gwabnan. Wannan sabani dai shi ne yayi sanadiyar faduwar jam’iyar a wannan lokaci.

Tabbas masana na ganin cewa wannan sabani da ya bullo kai a jam’iyar ta APC a wannan lokaci duba da irin mutanen da suke jagorantarsa hadi da har yanzu ba a san inda mataimakin gwamnan jihar, Nasiru Yusuf Gawuna ya sanya gaba ba ana ganin zai iya dilmiyar da jam’iyar a jihar.

Ita dai kanta maganar mataimain gwamna a jihar babbar magana ce inda masana harkokin mulki suke ganin tuntuni dai an ajiye shi a gefe inda ka dauko wadda ake tsammani zai yi masa mataimaki a baya wato kwamishinan kananan hukumomi, Murtala Sule Garo aka sanya gaba.

Zamu ajiye wannan batu a nan. Za kuma muci gaba da bibiya.

Kuna iya bibiyarmu ta kafafen sada zumuntarmu a

Facebook
YouTube
Instagram
Telegram
Ko kuma ku aiko mana da gyara ko shawara ta adireshinmu na email – Labarai24@yahoo.com

Ku shiga group dinmu don samun labaru kullum 👉 WhatsApp

Ali Sabo Dan Jarida Mai Sharhi Akan Al’amuran Yau Da Kullum. Za a iya samunsa ta aliyuncee@gmail.com

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan