Gwamnatin Najeriya Ta Saka Wa Twitter Sharuɗɗa Kafin Ta Buɗe Shi
Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ce sharuɗan da ta sa wa shafin Twitter kafin ta sake buɗe shi za su shafi dukkan kafafen sada zumunta na zamani a Najeriya.
Ministan Yaɗa Labarai da Al’adu, Lai Mohammed ne ya bayyana haka a wani shiri mai suna This Morning na gidan talabijin na TV Continental.
Ministan bai bayyana sharuɗan da Gwamnatin Tarayyar ta sa ba.

Ya ce za a miƙa wa Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari rahoton kwamitin sulhu da Twitter da Gwamnatin Tarayya ta kafa.
Lai Mohammed, wanda ya jagoranci kwamitin, ya ce tattaunawar da aka yi da Twitter ta yi ma’ana.
“Abin da zan iya cewa shi ne shawarwarin da za mu gabatar ba za su zama ga Twitter ba kaɗai amma za su shafi dukkan shafukan sada zumunta a Najeriya.
“A yau muna hukunta Twitter ne, ba ma son a ce gobe kuma muna hukunta Facebook da Instagram. Shawarwarinmu za su tattara komai.
“Za ku iya tuna cewa a lokacin Bikin Samun ‘Yancin Kai Karo na 61, Shugaban Ƙasa ya ce Twitter za ta dawo da zarar sun cika sharauɗɗan gwamnati”, in ji Lai Mohammed.
“Ko jiya da daddare, tawagar ministoci ta zauna a ƙarƙashin jagorancina mun kuma duba matsayin abubuwa.
“Ina so in ce ya kamata mu tsaya mu jira kwamiti ya bayar da rahotonsa a hukumance amma dai abubuwa suna yin kyau”, in ji shi.