Tuni dai tunanin ‘yan Nijeriya ke ci gaba da hasashen tare da kokwanton cewa yaushe Nijeriya za ta kawo ƙarshen matsalar harsken wutar lantarki a dai dai lokacin da ma’aikatun gwamnatin tarayya daban-daban a shekarar 2022 su ka ware biliyan 104 dan sayen Janareta da zai basu wuta da zuba masa mai a shekarar 2022.
A dadin kuɗaɗen da aka ƙiyasta sun zarta kuɗin shigar jihohi 24 a ƙasar.
Hakan dai na ƙunshene a cikin bayanan dake tattare a kasafin kuɗin Nijeriya na shekarar 2022 wanda majalisa ke tantan cewa zuwa yanzu.

Lamarin dai na ci gaba da tabbatar da taɓarɓarewar harkar samar da wutan lantarki a Nijeriya duk da maƙudan kuɗaɗen da ake zubawa wannan sashi da ya kai ga cefanar da wasu sassansu a hannun ‘yan kasuwa.
Wanda ko a shekara ta 2020 a ƙoƙarin gwamnatin na daƙile shigo da Janareta, ta sanya gabatar da ƙudirin da zai hana shigo da Janareta daga ƙasashen waje. Dokar da a lokacin ake hasashen zata taimaka wajen bunƙasa harkar wutar lantarki a Nijeriyar.
Har wa yau dai a lokacin ta kaiga hatta majalisar dokokin Najeriya na kasafta maƙuddan kuɗaɗe wajen shigo da Janaraito a ƙasar, amma har zuwa yanzu wannan doka bata kai ga cimma gaci ba.