An haifi janar Yakubu Gowon ne a garin Pankshin na Jos jahar Plato, ranar 19 ga watan Oktoban shekarar 1934.
Janar Gowon ya yi karatunsa a garin Zariya a jahar Kaduna, inda daga bisani ya shiga aikin soji.
Ya samu horan soji a kasar Ghana da Ingila, sau biyu kuma ya yi aiki a kasar Congo a rundunar wanzar da zaman lafiya ta Najeriya a kasar.
Janar Gowon ya yi gudun hijira zuwa kasar Burtaniya, kuma an sauke shi daga mukaminsa bisa zargin sa da hannu wajen kashe wanda ya gaje shi wato janar Murtala Ramat Muhammed a shekarar 1976.
A shekarar 1981 Alhaji shehu Shagari yai masa afuwa, sannan kuma a shekarar 1987, a lokacin mulkin janar Ibrahim Badamasi Babangida akai mayar masa da mukaminsa na soji.

Janar Yakubu Gowon ya yi karatun digirinsa na 3 wato Ph.D a jami’ar Warwick a Burtaniya, ya kuma zama Farfesa a jami’ar Jos.
Yanzu haka Janar Yakubu Gowon ya zama daya daga cikin dattawan Najeriya.
Wasu Daga Cikin Ayyukan Da Yakubu Gowon Ya Yi A Lokacin Mulkinsa
- Shirin ingantaka albashin ma’aikata wanda aka fi sani da Udoji.
- Ƙirƙiri hukumar bautawa ƙasa wadda ake kira National Youth Service Corps abar taƙaitawa da NYSC. Domin samar da haɗin kai a tsakanin matasan Nijeriya waɗanda suka kammala karatu a babbar makaranta, wanda kuma har zuwa yanzu nan shirin yana nan ana gudanar da shi.
- Gina garin FESTAC da ke babban birnin tarayya na lokacinsa wato Lagos.
- Gina gadoji da dama a garin Lagos da ma sauran sassan guraren da ake da buƙatar hakan a ƙasa. Wannan ta saka ake yi masa kirari da mai gina gada (The bridge builder).
- Gina katafaren ɗakin taro na ƙasa (National Theater, Lagos).
- Gina jami’o’i.
- Canja tsarin Nijeriya daga Yankuna huɗu;
Yankin Arewa, Yankin Yamma, Yankin Tsakiyar Yamma da Yankin Gabas (Northern Region, Western Region, Mid-Western Region and Eastern Region) zuwa jahohi goma sha biyu. Jahohin su ne: Jahar Arewa maso Yamma (North-Western State); Jahar Arewa maso Gabas (North-Eastern State); Jahar Kano; Jahar Tsakiyar Arewa (North Central State); Jaha Filato-Binuwai (Benue-Plateau State); Jahar Kwara; Jahar Yamma (Western State); Jahar Lagos; Jahar Tsakiya Yamma (Mid-Western State); Jahar Tsakiyar Gabas (East-Central State); Jahar Kudu Maso Gabas (South-Eastern State) da kuma Jahar Rivers. - Gina babban titin Ibadan zuwa Lagos.
- Kawo ƙarshen yaƙin basasar da aka ɗauki shekaru uku ana yi.
- Sake gina yankunan da yaƙin basasa ya ɗaiɗaita tare kuma da sake tsugunnar da ‘yan gudun hijirar da yaƙin ya kora daga gidajensu a ƙarƙashin shirin da aka kira Reconciliation; Rehabilitation and Reconstruction (The 3Rs) a Turance.
- Shirin miƙa mulki ga hannun farar hula. Duk da cewa shirin nasa bai kai ga nasara ba, amma dai Janar Gowon ya shirya miƙa mulki ga farar hula wanda ya sanar a shekarar 1970 bayan kammala yaƙin basasa.
- Sake tsarin rundunar sojijin Nijeriya.
- Aiwatar da tsarin ciyar da ƙasa gaba a aikace tare kuma da gyara ta’adin da yaƙi ya haifar.
- Kawar da ɓarna a rayuwar Nijeriya a mataƙin ƙasa.
- Sake ƙirƙirar wasu jahohi.
- Samar da sabon kundin tsarin mulki.
- Sake fitar da sabon salon rabon arziƙin ƙasa.
- Gudanar da Ƙidayar jama’ar ƙasa.
- Kafa ƙwararan jama’iyyun siyasa na ƙasa.
- Gudanar da zaɓe a matakan jahohi da na Tarayya.
- Ya taƙaita tsoma hannun kamfanonin waje a cikin harkokin gudanar da tattalin arziƙin Nijeriya a cikin shirinsa na indigenization policy.
- Gina babban birnin Tarayyar Nijeriya, Lagos zuwa matakin da ya amsa sunan birni a idon duniya.
- Kusanta Nijeriya da ‘yan’uwanta ƙasashen Afirka tare kuma da ɗaukaka darajarta a tsakaninsu da har ta kai da amsa sunanta na Uwa ma bada mama a Afirka.
- Kai Nijeriya matsayi na tara a harƙar fitar da manfetur zuwa kasuwannin duniya.
- Jagorantar kafuwar ƙungiyar ECOWAS a 1975.