Kanywood Maja Sun Ziyarci Fadar Gwamnatin Kano: Ganduje ya sakawa Iyantama Albarka

504

Fitattun jarumai a masana’antar Kanywood masu ra’ayin APC Gandujiyya sun kaiwa gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje wata ziyarar godiya tare jaddada goyon bayansu ga gwamnatin.

Tun da farko jarumi Mustapha Naburaska ne ya wallafa sanarwar ziyarar tare da hotunan jaruman a shafinsa na Instagram, inda a cikin ɗaya daga cikin hotunan an ga yadda gwamna Abdullahi Umar Ganduje ke dafa kan shahararren Fardusa na fina-finan Hausa, Alhaji Hamisu Lamido Iyantama.

Lokacin da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ke sanyawa Hamisu Iyantama Albarka

Idan za a iya tunawa dai a cikin watan Satumbar da ya gabata ne Jarumi Mustapha Naburaska ya ce ya ajiye Jar Hularsa Saboda ba gadar ta ya yi ba. Inda ya ce yanzu ya rungumi tafiyar Ganduje ka’in da na’in saboda a cewar sa ban da jihar Lagos babu inda ake zuba aiki kamar jihar Kano.

Sauran jaruman da su kai ziyarar fadar gwamnatin Kano sun haɗa Sulaiman Bosho da Kabiru Maikaba da Shehu Hassan Kano da Hajara Usman da Hadizan Saima da sauran fitattun jarumai a masana’antar ta Kanywood.

Jaruman Kanywood Maja tare da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje

A shekarun baya dai ba kasafai ake ganin jaruman na Kannywood suna fitowa su nuna alkibilarsu a siyasance ba, amma a baya-baya nan lamarin ya sauya.

Akan gan su sun yi kwamba suna kai wa ‘yan takara ziyara, su kuma hada kai su yi masu wakoki daban-daban, abinda kan haifar da rarrabuwar kawuna a tsakaninsu.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan