Yau ake bukin Mau’ludin fiyayyen halitta Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam

358

A yau ne ake gudanar da bukukuwan mauludi a Najeriya da wasu kasashen musulmi na duniya ,domin tunawa da ranar da aka haifi manzon Allah SAW.

Yau din dai rana ce ta hutu a Najeriyar, rana ce kuma da musulmi ke gudanar da adduo’i da kuma bukukuwa domin muhimmancin ta.

Al’ummar Musulmi da dama ne yau a faɗin duniya ke murna da zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammadu (Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.)

Musulmai da dama sun yi amannar cewa a watan Rabiu’l Awwal, aka haifi Annabi Muhammadu (SAW).

A irin wannan rana ce Allah (SWA), ya yi wa halittarsa kyautar da ta fi kowacce irin kyauta daraja wato Manzon Allah SAW, kamar yadda Musulunci ya bayyana.

Wani ɓangare na gurin Maulidi a jihar Bauchi

Malamai sun ce al’ummar Musulmai za su iya yin dukkan abin da suke gani Allah da Manzonsa sun yarda a yi, sai su yi domin nuna murnarsu da zagayowar wannan rana.

Al’ummar Musulmai dai kan yi hidima a wannan lokaci, inda makarantun allo ko na Islamiyya kan shirya mauludi ta hanyar ƙayata waje a gayyaci manyan baƙi a zo a bai wa ɗalibai karatu da waƙoƙi na yabon Annabi su zo su rinƙa yi.

Wata al’ada kuma za ka ga a wannan rana a kan dafa abinci da nama musamman kaji a raba gida-gida na maƙwabta kamar ranar sallah.

A wani lokaci ma har ɗinki ake yi wa yara don su sanya sabon kaya kamar sallah.

Ga wasu mutanen kuma a kan shirya taron lakca inda za a gayyato malamai su yi wa’azi.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan