Uwar jami’yyar APC ta ƙasa ta tabbatar da zaɓen Abdullahi Abbas – Ganduje

377

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar ya bayyana cewa uwar jam’iyyar APC ta ƙasa ta tabbatar da zaɓen da aka yi wa Abdullahi Abbas a matsayin sahihin zaɓe daga jihar Kano.

Gwamna Ganduje ya bayyana hakan ne a zaman majalisar zartarwa da ya gudana a yau Laraba, kamar yadda mai taimaka masa akan harkokin shafukan sadarwa na zamani Abubakar Aminu Ibrahim ya sanar a shafinsa na facebook.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje

Wannan dai yana zuwa awanni da ɗan majalisar dattawa mai wakiltar mazabar Kano ta tsakiya, kuma tsohon gwamnan jihar, Mallam Ibrahim Shekarau ya kafe cewa Alhaji Ahmadu Haruna Zago shi ne shugaban jam’iyyar APC zababbe na jihar Kano.

Malam Ibrahim Shekarau ya jaddada wannan matsayi nasa ne a wata sanarwa da ya fitar, sakamakon rabuwar kai da aka samu a zaben shugabannin jam’iyyar da ka yi a ranar Asabar 16 ga watan Oktoba, 2021, inda aka yi zabe bangare biyu, wanda kuma har kawo yanzu uwar jam’iyyar ta kasa ba ta fitar da wata tartibiyar sanarwa kan shugabancin da ta amince da shi ba.

A ranar Asabar ɗin da ya gabata bangaren gwamnan jihar Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya zabi tsohon shugaban jam’iyyar wanda kuma har lokacin zaben yake matsayin shugaban riko, a matsayin sabon shugaban jam’iyyar, yayin da bangaren Ibrahim Shekaru ya zabi Alhaji Ahmadu Haruna Zago a matsayin shugaban.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan