Fasto Olayide Babatunde na Cocin Glorious and Divine Calling Ministry dake Ayobo a jihar Legas ya kira da a riƙa yi wa ‘yan sandan Najeriya gwajin ƙwaƙwalwa.
Mista Babatunde ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN, ranar Laraba a Legas.
A cewarsa, ya kamata gwamnati ta kafa cibiyoyi inda ‘yan sanda za su riƙa zuwa ana gwada lafiyar ƙwaƙwalwarsu kafin su fara aiki.

“Wasu ‘yan sandan suna da zane a bayansu kuma suna yawo da injin cirar kuɗi na POS, suna kama matasa masu yawa a motoci masu baƙaƙen gilashi.
“Da yawansu sukan sha wiwi kafin su fara aiki kuma hakan ya ɓata na gari da suke cikinsu.
“Kuma ya kamata gwamnati ta yi wa kowane ɗan sanda gwajin jini, kuma duk da ya ƙi yin gwajin a kore shi.
“Akwai matasa da yawa masu hankali da suka gama karatu ba su da aikin yi waɗanda a shirye suke su yi wa ƙasar nan aiki”, in ji shi.
Da yake bayyana ra’ayinsa game da zanga-zangar EndSARS da aka yi a 2020, Mista Babatunde ya ce zanga-zangar ta karya lagon ‘yan sanda.
A cewarsa, ‘yan sanda sun zama suna tsoron jama’a, kuma ba sa so a danganta su da aikin ɗan sanda.
“Misali, idan kai ƙara caji ofis, sai ɗan sanda ya ce maka ka je gida ku sasanta.
“Sukan tambayi waɗanda suka kawo ƙara cewa: “Ba ku ne kuka ce ba kwa son ‘yan sanda ba”, ya ƙara da haka.