HOTUNA: Sama da Dakarun Hukumar Hisbah Dubu Tara ne su ka Gudanar da Faretin girmamawa a Ranar Hisbah

271

Sama da dakarun Hukumar Hisbah dubu tara ne su ka gudanar da faretin girmamawa domin nuna farin cikin a bikin ranar Hukumar Hisbah ta wannan shekara.

Bikin na bana wanda aka gudanar dashi haɗe da kaddamar da sabbin dakarun sakai na hukumar wato (Hisba Marshell) da kuma sabbin kayayyakin sawar dakarun Hukumar na Union.

A jawabin daya gabatar yayin taron wanda aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha da ke Kofarmata da maraicen wannan rana ta Alhamis 21 ga OKtoba, 2021, gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya jinjinawa dakarun Hukumar Hisbah bisa rawar gani da su ke takawa wajen tabbatar da ɗa’a da kuma kare dokokin Ubangiji.

Wasu daga cikin dakarun Hisbah

Ya kara da cewa gwamnatin jihar Kano, ta himmantu akan sha’anin Hukumar ta Hisbah ta hanyar samar da kayayyakin aiki na zamani da sauran abubuwan da hukumar ke buƙata.

A jawabin shugaban Hukumar Hisbah ta jihar Kano, Ustaz Harun Ibni Sina, ya buƙaci gwamnatin jihar Kano, ƙarƙashin gwamna Abdullahi Umar Ganduje, da ta samar da ƙarin dakarun Hukumar daga a dadin dakarun da Hukumar ke da su ɗari tara zuwa abunda ya sawwaƙa.

Ibni Sini, wanda ya yabawa gwamnatin Kano ƙarƙashin gwamna Ganduje bisa amincewa Hukumar ta samarda ƙarin dakarun saka kai su dubu biyar da ɗari bakwai a dukkanin masarautun jihar Kano guda biyar tare da yin albishir ga dakarun Hisbah kan cewa gwamnatin Kano, ta amince ayi ƙarin girma ga dakarun hukumar ta Hisba tun daga wannan rana.

Dakarun Hisbah Ya yin fareti

Anasa bangaran shugaban hukumar Hisba ta jihar Kano Ustaz Ibrahim Shehi Shehi mai hula ya godewa gwamnatin jihar Kano bisa samarda tsare-tsaren ci gaban Hukumar tare da buƙatar gwamnatin Kano, da ta yi ƙarin Albashi ga dakarun hukumar tayanda zasu ƙara samun kwarin gwiwa akan ayyukan gina Al’umma da suke gudanarwa.

A taalikin daya gabatar kan ayyuka da dalilan da suka sanya aka samar da hukumar Hisbar tun asali, Shehin Malami Farfesa Umar Sani Fagge, yace ya zama wajibi ga dukkanin mai amsa sunan ɗan Hisbah ya kiyaye da dukkanin martabobin da hukumar ta kafu akansu domin kare martabar addinin Allah.

Ibni Sina Tare da Gwamnan Kano Ganduje

Daga karshe an gudanarda kasidu da wasannin fadakarwa tare da faretin da dakarun Hukumar za su riƙa gabatarwa a hukumance.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan