ILIMI: Saura Ƙiris Kwalejin Sa’adatu Rimi ta Koma Jimi’a – Ganduje

392

Gwamnatin jihar Kano tace shirye shirye sunyi nisa game da batun ɗaga darajar kwalejin ilmi ta Sa’adatu Rimi zuwa matakin Jami’a.

Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje shi ne ya tabbatar da hakan yayin wata ziyara da shugabanin kwalejin su ka kai fadar gwamnatin jihar Kano, ƙarƙashin shugaban kwaleji Farfesa Yahaya Isa Bunkure.

Dakta Abdullahi Ganduje, ya ce tuni tuntuɓa ta yi nisa tsakanin gwamnatin Kano da hukumar kula da jami’o’i ta ƙasa NUC akan batun ɗaga dajar kwaleji zuwa jami’a.

Yana mai bayyana kwalejin a matsayin kwalejin ilimi ta biyu a cikin tsofaffin kwalejojin ilimi da su ke a yankin Arewacin ƙasar nan baya ga tsohuwar kwalejin horon malamai ta Kano, da a yanzu take jihar Jigawa Wato (Gumel Advance teacher College)

Ya ce kwalejin tana da dukkanin abubuwan da ake buƙata na sharuɗɗan zama jami’a tun daga matakin malamai da kayayyakin aiki da sauran abubuwan da ake buƙata a jami’a.

Da yake tsokaci kan darussan bada horo afannin ilimin koyarwar da kwalejin ke gudanarwa a matakin shaidar ilimin koyarwa ta Kasa wato NCE, gwamna Ganduje yace tuni gwamnatin Kano ta tsara yanda za a samarwa darussan matsuguni a manyan makarantun gwamnatin Kano dake gudanarda darussan bada horon ilimin koyarwa.

Tunda farko shugaban kwalejin ilimin ta Sa’adatu Rimi dake Kumbotso, Farfesa Yahaya Isa Bunkure ya bayyana wa majalisar zartawa ta Kano, cewa sunzo fadar gwamnatin Kano ne domin sanarwa gwamna da majalisar zartawa ta Kano matsayin da kwalejin ta kai tare da bukukuwan cikar kwalejim shekaru 40 da kafuwa.

Farfesa Yahaya Bunkure, har ila yau ya yi amfani da lokacin ziyarar wajen tabbatarwa da gwamnatin Kano ci gaban da kwalejin ke samu a ɓangaren bada shaidar matakin ilimin Digiri da kwalejin ke bayarwa dama sauran manyan takardun shaidar ilimi daban daban.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan