Allah Buwayi: Abubuwan Ban Mamaki Game da Halittar Jemage

393

Jemage wata halittar Allah ce mai matukar ban mamaki. Jemage dabbace dake kama da tsuntsu (amma ba tsuntsu ba ne). Yana da fuka-fukai guda biyu da yake tashi sama dasu tamkar tsuntsu. Gaba ɗayan rayuwar jemage a sama yake yinta.

Girman jikin riƙaƙƙen jemage bai fi na kwatankwacin ɗan matsakaicin ɓeran gida ba, sauran duk girman fukafukin ne. Yana da ƴar gajeriyar jela da ƙafafu guda biyu yan ƙanana wadanda suke dauke da yatsu masu ƙarfi don riƙe reshen bishiya. JEMAGE shi kadai ne dabba ‘mai shayarwa’ (wacce yanzu aka sani sananniya) dake iya tashi sama.

Jemage

Kansa, idanunsa, hancinsa da bakinsa irin na dangin ɓeraye ne “rodents”. Yana da haƙora ƙananu masu kaifi guda 38 a cikin bakinsa. Akwai kuma Jemagen da ake kira da “VAMPIRE BAT” yana da haƙora 20 ne kacal. Jemage yana da sauri a sararin sama, domin akwai wanda ya kanyi tafiyar murabba’in kilomita 120 cikin awa guda.

Jemage baya sauka ƙasa. Yana rayuwarsa kacokan a saman bishiyoyi. Idan zai yi barci yana kama reshen bishiya da ƙafafunsane ya sakko da kansa ƙasa kana sai ya rufe gangar jikinsa da kansa da fukafkansa (roosting).

Mafi yawanci abincinsa basa wuce ƙwari, tsutsotsi da yayan itatuwa (fruits). Jemagu basa shan ruwa. Ruwan dake cikin abincinsu ya ishe su. Suna yawo su nemi abinci da daddare ne kawai (nocturnal).

Jemage

JEMAGE ɗaya yakan auri mata da yawa (polygyny). Macen JEMAGE tana ɗaukan ciki ta haihu maimakon ƙwai da wasu tsuntsaye ko dabbobi suke yi ba. Bayan ta haihu ta reni ɗiyan ta hanyar shayarwa (tana da nonuwa).

Jemage shi kaɗai ne dabba mai shayarwa dake iya tashi sama. Jemagu suna da dubura wacce ta nan suke kashi (ba ta baki ba kamar yadda Hausawa suke ikirari), sannan suna da wajen da suke yin fitsari da jima’i.

Asalin rubutu daga Arewa Genius Hub

Kuna iya bibiyarmu ta kafafen sada zumuntarmu a

Facebook
YouTube
Instagram
Telegram
Ko kuma ku aiko mana da gyara ko shawara ta adireshinmu na email – Labarai24@yahoo.com

Ku shiga group dinmu don samun labaru kullum 👉 WhatsApp

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan