Tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa bai san gwamna Abdullahi Umar Ganduje na aike masa da sakon murnar zagayowar ranar haihuwar sa ba.
Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya bayyana hakan ne a cikin wata tattaunawa da ya yi da sashen Hausa na BBC a yau Asabar.
Tun da farko an tambayi Rabi’u Kwankwaso kan ko ya ga sakon taya murnar cikarsa shekara 65 da gwamnan Kano mai ci Abdullahi Umar Ganduje ya aika masa ?, sai Kwankwaso ya ce bai gani ba domin aiki ya masa yawa.
”Ina ta aikace-aikace ban sani ba, in da haka yake tun da farko da ba haka ba, duk wanda ya sanni ba wanda zai zo ya ce ya fadi wani abu a kan Ganduje na saurare shi, domin dukkaninsu Kwamishinoni sun sani da sauran ma’aikata da mutan gari, domin idan kace mutum yana da laifi daya amma yana da dai-dai guda tara sannan kace za ka kalle shi da wannan laifin ai ka ga akwai matsala”.

Ya ƙara da cewa ”Na zauna da mutane lafiya ciki har da Ganduje, haka muka bar gwamnati muka koma ma’aikatar tsaro, haka muka yi tsari ya tafi Chadi, haka kuma yana can na ce ya sauka ya dawo gida mu yi aiki da shi, ya dawo na dauki fom din mataimakin gwamna na bashi, na ce kai ne babba, ba tare da ko sisin Kwabo ba, domin mu a tsarinmu na Kwankwasiyya ba wanda zai ce ka bada ko sisin Kwabo”
Sai dai Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi zargin cewa duk da waɗannan alherai da ya yi wa tsohon mataimakin nasa, sai ga shi a yanzu shi da shi ya fi adawa a kan kowa.
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje dai ya karbi mukamin gwamnan daga hannun Rabi’u Musa Kwankwaso, kuma shi ne ya yi wa Kwankwason mataimakin gwamna a farko daga shekarar 1999 zuwa shekara 2003 sannan daga shekara 2011 zuwa 2015.
Haka kuma Kwankwaso da Ganduje sun kwashe shekaru da yawa suna siyasa kafin su raba gari a cikin shekarar 2016, wanda hakan ne ya tilasta Kwankwason ficewa daga jam’iyyar APC.