Gobara Ta Ƙone Muhimman kayayyaki na Miliyoyin Naira a Jami’ar Bayero Ta Kano

418

Wata gobara wadda ta yi sanadiyyar rasa wasu muhimman kayayyaki ta tashi a ginin gwaje-gwaje na sashen Bio-Chemistry da yake a tsohuwar jami’ar Bayero.

Wani ɓangare na gobarar

Gobarar dai ta jawo asarar wasu muhimman kayayyaki na maƙudan kuɗaɗe kamar yadda Jaridar Daily Reality Hausa ta tabbatar.

Da yake zantawa da wakilin jaridar TDR Hausa, wani ma’aikacin wajen da ya nemi a ɓoye sunansa, ya ce a gaskiya ma’aikatan wajen suna ƙoƙari wajen kiyayewa, duk da cewa ya fuskanci suna yawan barin wutar lantarkin wajen a kunne, ko da kuwa da daddare ne. Ya bayyana cewa wajen yana ƙunshe da injina da abubuwa na miliyoyin nairori tare da samfurin ayyukan ɗalibai iri-iri.

Tuni dai shugaban jami’ar, farefasa Sagir Adamu Abbas ya hallara a wajen da kansa domin ganewa idonsa irin ɓarnar da gobarar ta yi, tare da jajantawa ma’aikatan da abin ya rutsa da su, gami da ƙoƙarin samo hanyoyin da za a kawo gyara da kuma daƙile faruwar hakan a gaba.

Rahoton Daily Reality Hausa

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan