Jam’iyyar APC ta ƙasa ta tabbatar da zaɓen Abdullahi Abbas

332

Kwamitin jin korafin zabe da uwar Jam’iyyar APC ta turo Kano ya nuna bai san da wani zabe ba, bayan zaben da bangaren gwamnati karkashin Jagorancin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje suka yiwa Abdullah Abbas a matsayin shugaban jamiyyar APC reshen jihar Kano.

A satin da ya gabata ne aka gudanar da zaben shugabannin jam’iyyar APC na jihohi, inda a jihar Kano da sauran jihohi aka samu rarrabuwar kai.

Shugaban Jam’iyyar APC na jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas Sanusi

An dai sa zare tsakanin Gwamna Ganduje da bangaren tsohon Gwamna Sanata Shekarau, har ta kai da kowanne tsagi ya yi zaben sa dabam. A yayin da tsagin gwamnati ya gudanar da zabensa a dakin wasanni na ‘Indoor’, shi kuma tsagin Shekarau ya gudanar da nasa zaben a garin Janguza.

Sai dai a karshen makon nan, uwar jam’iyya ta turo tawaga mai mutum biyar, karkashin jagorancin Mr Tony Macfoy don jin korafin zaben.

Mr Macfoy ya ce zaben da aka yi a dakin wasanni na ‘Indoor’ shi ne halastacen zabe, don haka ba zai karbi korafi akan zaben da aka yi a wani wuri ba.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan