Kwamitin Kwankwasiyya Na Soshiyal Midiya: ‘Makaho zai jagoranci Masu Ido’

417

A yau Asabar tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya ƙaddamar da wani kwamiti wanda zai lura da ƴan Kwankwasiyya masu amfani da shafukan sadarwa na zamani wato “Kwankwasiyya Social Media Leading Committee, ƙarƙashin jagorancin Malam Muhammed Tajo Othman.

An ƙaddamar da kwamitin ne bayan Kammala wata lakca da gidauniyar ilimi ta Kwankwasiyya ta shirya tare da haɗin gwiwar rukunin masana masu aƙidar Kwankwasiyya su ka shirya domin taya murnar ga jagoran na Kwankwasiyya cika shekaru 65 da haihuwa.

Dakta Saminu Umar a lokacin da ya ke gabatarwa da ƴan Kwankwasiyya lakca akan soshiyal midiya

Kwamitin na Kwankwasiyya Soshiyal Midiya yana ƙarƙashin shugabancin Malam Muhammed Tajo Othman, wanda tsohon ma’aikaci ne a hukumar hana fasa ƙwauri ta ƙasa. Haka kuma Muhammad Tajo ya taɓa yin takarar majalisar wakilai a mazabar Minjibir da Ungogo a shekarar 2019.

Shugaban Kwamitin Soshiyal Midiya na Kwankwasiyya, Malam Muhammed Tajo Othman

Sauran mambobin kwamitin sun haɗa da Yusuf Sharada da Dr. Farouk Kurawa da Farfesa Umar Farouk Jibrin, da Hon Saifullahi Hassan da Rabi Hotoro, da Hon. Abbas Sani Abbas, da kuma Hon. Rabi’u Saleh Gwarzo.

Tuni al’umma a jihar Kano su ka fara tofa albarkacin bakinsu dangane da yadda aka danka ragamar shugabancin wannan kwamiti a hannun tsohon jami’in tsaro bayan kuma ga Farfesa a harkokin sadarwa da yaɗa labarai wanda su ke ganin shi ne mafi dacewa ya riƙe kwamitin.

Farfesa Umar Farouk Jibrin tsohon shugaban sashen koyar da aikin jarida na jami’ar Bayero da ke Kano

A cikin masu ƙalubalantar shugabancin kwamitin akwai fitaccen ɗan jaridar nan kuma babban editan jaridar Daily Najeriya, Malam Jaafar Jaafar, inda ya wallafa wani rubutu a shafinsa na facebook jim kaɗan da ƙaddamar da kwamitin.

Jaafar Jaafar ya ƙalubalanci yadda tsohon jami’in kwastan zai shugabanci abin da ba shi da ƙwarewa akai bayan ga mutumin da ya kai matakin Farfesa a harkar sadarwa da kuma aikin jarida.

“An naɗa tsohon jami’in hukumar kwastan wanda ba a cika ganin motsinsa a shafukan sadarwa na zamani ba a matsayin shugaban kwamitin soshiyal midiya na Kwankwasiyya, inda kuma Farfesa akan harkokin sadarwa wanda ya shafe shekaru 35 yana koyar da aikin jarida, har ta kai ga ya rike sashen koyar da aikin jaridar dungurungum ya kasance mamba a cikin kwamitin. Wannan abin mamaki da yawa ya ke! Ina matasaaa?” In ji Jaafar Jaafar.

Lokacin da ake ƙaddamar da kwamitin

Ƴan siyasa dai na amfani da amfani da matasa wajen yaɗa manufofinsu da tallansu a shafukan sadarwa na zamani, inda galibin al’umma ke dogaro da kafafen sada zumuntar, wadanda aka fi sani da social media wajen samun labaran da su ka shafi siyasa da sauran labaran duniya.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan