Najeriya Na Dab Da Fara Amfani Da Sabuwar Naira Ta Intanet

451


A ranar Litinin, 25 ga Oktoba, 2021, Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari zai ƙaddamar da Nairar Intanet wadda Babban Bankin Najeriya, CBN, ya samar mai suna eNaira a Fadar Shugaban Ƙasa, Abuja.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Jami’in Huɗɗa da Jama’a na CBN, Osita Nwanisobi, ya fitar ranar Asabar.

Ƙaddamar da wannan naira ta Intanet ya samu ne sakamakon wani dogon nazari da CBN ya yi da nufin bunƙasa hanyoyin hadahadar kuɗi da kawo sauƙi a harkokin kuɗi.

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari

Sanarwar ta ce biyo bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki da suka haɗa da ma’aikatan banki, masana kuɗin Intanet, ‘yan kasuwa da kuma wani sashi na ‘yan Najeriya, CBN ya tsara wannan kuɗi.

eNaira, a cewar CBN, yana alamta wani mataki na ci gaba a harkar kuɗi a Najeriya.

Sanarwar ta ƙara da cewa CBN zai jajirce wajen gani eNaira ɗin ta karɓu, kamar yadda naira ta fili ta karɓu.

CBN zai ci gaba da aiki da masu ruwa da tsaki don tabbatar da cewa kowa yana jin daɗin aiki da eNaira ɗin, musamman mazauna karkara da mazauna birane inda ake da bankuna, a cewar sanarwar.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan