Ɗan shekaru 25 ya fito neman shugabancin matasan Jam’iyyar PDP a Najeriya

739

Muhammad Kadade Suleiman matashi daga jihar Kaduna ya fito neman shugabancin mukamin matasan Jam’iyyar PDP a zaben shugabannin jam’iyyar da za ai a mako mai zuwa.

Kadade Suleiman wanda ya bayyana cewar a matsayinsa na matashi zai yi kokarin ganin ya kawo sauyi a cikin lamuran matasan jam’iyyar PDP wajen ganin ana damawa da su a cikin dukkan lamuran Jam’iyyar.

Muhammad Kadade Suleiman

Tuni dai uwar jam’iyyar ta kasa ta ware kujerar shugaban matasan jam’iyyar PDP ga jihar Kaduna, inda yanzu haka ake da matasa guda biyu da suke nuna sha’awar neman wannan kujera ta shugabancin matasa.

Ba kasafai dai ake ganin fuskokin matasa suna neman manyan mukamai irin wannan ba, a baya dai ansha ganin mutane masu shekaru sama da sittin na neman mukamin shugabancin matasa a cikin jam’iyyar ta PDP, shin ko fitowar matashi Muhammad Kadade Suleiman yana alamata cewar Jam’iyyar PDP ta fara kawo sauye sauye a cikin lamuran gudanarwarta?

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan