Fitila: Sharhin Manyan Rahotannin Makon Jiya

391

Makon da muka yi ban kwana da shi an samu muhimman labaru wadanda dukkanin al’umma na kasashe masu tasowa musamman Africa ya kamata su dauki izina akansa sannan su yiwa kansu karatun ta natsu don gudun faruwar hakan a nan gaba.

A ranar 20 ga watan Oktoba na shekarar 2011 ne wasu masu fafutakar tabbatar da dimukuradiyya a kasar Libya suka sami damar kashe tshohon shugaban kasar bayan safe watanni suna zanga-zanga kan neman shugaban yayi murabus ya mika mulkin kasar a hannun farar hula.

Wannan al’amari dai ya faru a kusan dukkanin kasashen gabas ta tsakiya inda shuwagabanni da dama suka rasa kujerunsa wasu ma harda rasa rayukansu. Shi dai Muhammad Gaddafi shugaba ne wanda yayi kaurin suna wajen gina al’ummarsa ta bangarori da dama, kama daga harkar ilimi, lafiya, harkar sufuri da gidaje dama kowanne fanni na rayuwa.

Wannan ne yasa a waccan lokacin dan kasar Libya baya sha’awar zaman kowacce kasa kuma da yawansu basa wani aiki saboda abubuwan more rayuwar da marigayi Gaddafi ya samar a kasar. Rahotanni sunyi nuni da cewa, a kasar Libya ne kawai ake raba ribar man fetur (wadda shi ne babban hanyar samun Kudin kasar) ga dukkanin al’ummar kasar, harda kwa jaririn da aka haifa.

Duk da wadannan abubuwan more rayuwa da shugaba Gaddafi ya samar a wannan kasa sai ga shi an sami wasu gungun matasa sunyi masa bore wanda har ta kai ga rasa rayuwarsa. Mai karatu musamman dan Najeriya zai yi mamaki kuma zai tambaya duba da irin bakin mulkin zalunci da yake ciki kan yaya mutanen da ake yi musu wannan hidimar zasu yi bore ga shugabansu.

Babban abin lura anan shi ne, shugabanni na kasashe masu tasowa musamman Afrika da kasashen labarawa suna da sun mulki da son dadewa kan kujerun iko, wadda wannene yasa wasu lokutan ko da kuwa shugaban yanayin abinda ya dace za’a gaji da shi domin a halayyar dan Adam yana son canji kuma ba ya son abu musamman shugabanci ya jima a hannun mutum daya.

Sai dai wani hanzari ba gudu ba, ya kamata al’umma a ko da yaushe in zasu yi wani al’amari su rinka aunawa domin kar azo ayi da na sani daga baya kamar yadda al’ummar kasar Libya sukeyi yanzu. Sai muyi duba da alakar mutuwar shugaba Gaddafi da kuma tababbarewar tsaro a yankunan Sahel, tun bayan mutuwar Gaddafi harkokin tsaro a wannan yanki suka kara tabbabarewa a kasashe irinsu Najeriya, Chad, Niger, Cameroun da sauransu.

Masana harkokin tsaro sun alakanta wannan abu da mutuwar Gaddafi domin suna gani cewa bayan mutuwarsa makamai da kasar ta mallaka sun fada hannun daidaikun mutane wadanda basu da alaka da mallakarsu. Wannanne yasa yan ta’adda suka rinka samun makamai ta hannun wadannan mutane har suka fi karfin da suke tunkarar gwabnati.

Sai batu na gaba, a wannan makon da muka yi bankwana da shi ne dai shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan tare da mai dakinsa Emine suka kawo wata ziyara kasar nan, shugaban wanda ake ganin yana daya daga cikin shuwagabanni masu fada aji a duniya ya kawo ziyarar ne domin kara kulla alaka da kasar tare da inganta harkokin kasuwancin kasashen guda biyu da kuma hanyar tsaro.

A baya dai in zamu iya tunawa kasar ta Najeriya da Turkiya sun dan shiga wani yanayi na rashin jituwa lokacin da shugaba Erdogan ya bukaci da Najeriya ta kulle dukkanin wasu harkokin kasuwanci na wani shareren dan kasuwar kasar Turkiya wanda ake zargi da hannu dumu-dumu wurin kokarin yin zuyin mulki ga shugaban Recep wanda Najeriya taki amincewa da yin hakan.

Ziyarar ta bawa masana harkokin diflomaciya mamaki kwarai da gaske ganin yadda shugaban na Turkiya ya dauki yunkunrin juyin mulkin da akayi masa da muhimmacin gaske. Sai dai wasu na ganin cewa wannan ba komai bane in muka yi duba da yadda kasar ta Turkiya take kokarin samun kawaye a duniya domin tabbatar da karfin ta, da fadada kasuwanci ta sai kuma uwa uba kawayen da zasu tallafa mata a majalisar dinkin duniya domin cimma maradunta.

A ziyar dai an rawaito cewa shuwagabannin biyu sun amince suyi aiki tare da tallafawa juna a bangagori da dama ciki harda harkokin tsaro wanda ya dade yana cima kasar Najeriya tuwo a karya. Sai batu nagaba wanda yake jibi da harkokin tsaro, bayan labaru da hukumar tsaro ta kasar ta fitar a mabanbantan lokuta game da nasarar da take samu akan yan ta’adda tare da yan fashin daji cikin harda kisan shugaban Kungiyar Islamic State of West Africa Province (ISWAP) Abu Musab Al-Barnawi tare da wanda ya gaje shi wato Malam Bako.

Amma wani hanzari ba gudu ba, a lokacin da hukumar tsaro ke fitar da irin wadannan bayanai miliyoyin al’umma musamman wadanda suke zaune a yankunan Sokkoto, Zamfara, Katsina da Kaduna al’amari ba haka yake ba. Ranar Lahadin data gaba (17/10/2021) da misalign karfe hudu da rabi na yamma yan bindiga suka dirarwa al’umma a kasuwar Goronya dake jihar Sokkoto inda suka kashe mutane fiye da sittin.

Shaidun gani da ido sun shaidawa manema labarai cewa yan bindigar sun shafe fiye da awa biyu suna gudanar da barnar ba tare da an sami dauki daga jami’an tsaro ko daya. Irin wadannan hare-hare dama wasu tabbas suna kara saka shakku a zuciyar al’umma kan ko da gaske gwamnatin take wurin magance wannan matsala.

Al’umma na ganin cewa gwamnatin tafi mai da hankali wurin tallafawa wadanda abin ya shafa da dan abinda bai kai ya kawo ba bayan anyi musu barna fiye da kare rayukansu da dukiyoyinsu kamar yadda jaridun kasar suka rawaito ciki harda wannan jarida cewa hadaddiyar kungiyar gwamnonin kasar ta kai wata ziyara jihar ta Sokkoto domin jajantawa al’ummar jihar tare da bayar da tallafin Naira miliyan ashirin.

Sai batun da zamu rufe wannan shafi da shi, a wannan makon ne tsohon gwannan jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso yake murnar cika shekara sittin da biyar a duniya. Sanatan da ya mulki jihar tsohon shekara takwas daga shekar 1999 zuwa 2003 sai kuma 2011 zuwa 2015 ya kaddamar da aiyuka da dama musamman ta bangaren tallafawa matasa a harkokin ilimi.

Ana ganin dai tsohon gwamnan yana da matukar tasiri akan siyasar jihar Kano har ma da kasa baki daya duba da yawan mabiyansa musamman matasa, sai dai wasu na ganin cewa farin jinin Madugun Darikar Kwankwasiyar da kuma karfin ikonsa ya fara dishashewa duba da yadda yanayin siyarsa yake canjawa yanzu.

Muna addu’ar Allah ya albarkaci rayuwarsu domin anfanar da al’umma baki daya.

Kuna iya bibiyarmu ta kafafen sada zumuntarmu a

Facebook
YouTube
Instagram
Telegram
Ko kuma ku aiko mana da gyara ko shawara ta adireshinmu na email – Labarai24@yahoo.com

Ku shiga group dinmu don samun labaru kullum 👉 WhatsApp

Ali Sabo Dan Jarida Mai Sharhi Akan Al’amuran Yau Da Kullum. Za a iya samunsa ta aliyuncee@gmail.com

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan