FLUBOT: Sabuwar annobar waya

    389

    A farkon shekarar nan kamfanin F-Secure ya gargadi masu hulda da shi musamman na yankin nahiyar Turai akan bayyanar wata sabuwar manhajar satar bayanai mai suna Flubot.

    Suka ce, manhajar idan ta samu kutsawa cikin wayarka bata fita ta dadin rai. Kuma tana iya satar bayanai kai tsaye tare da aikawa mutane sakonni barkatai gami da fafake asusun mutum idan ta samu dama.

    Ana samun ta ne daga sakon SMS da ake aikowa mutum kamar daga wani babban kamfani cewar ya latsa likau din da ke tare da sakon domin ya amfana. Daga zarar ta shiga cikin wayar take soma aiki nan take.

    Sannu a hankali manhajar ta gangaro nan kasar, kuma duk da jan kunnen da hukumomi suka yi, tuni ta fara samun galaba ga dumbin masu amfani da wayoyin android.

    Yawancin wannan baƙar manhaja na da siffofi kamar haka:

    1. Tana iya sajewa da manhajar wani kamfani ko bankin da ke wayarka. Domin ka shigar da bayananka a aikawa masu aiko ta.
    2. A farko tana zuwa ne da siffar sakon SMS kamar wanda ke sama din nan.
    3. Tana iya kwafar lambobin wayarka ta tura musu irin sakonnin. Kuma a kudin wayrka za a biya.
    4. Tana iya kulle maka waya ta gagara sarrafuwa.
    5. Tana iya canja kamanni yadda ka san hawainiya.

    Maganin wannan manhaja ta Flubot shi ne:

    1. Da zarar ka ga sakon da baka amince da shi ba, maza goge shi.
    2. Kada ka latsa likau din da ke cikin sakon har sai ka tantance. Ko da shugaban MTN kwanaki ya aikawa mutane sakonni, daga bisani an samu wani nauin Flubot da ya kwaikwayi sakon yana aikawa masu tsautsayi.
    3. A guji saka manhaja kowacce iri musamman wadanda ba sa kundin Google Playstore.
    4. A rika yawaita ajiye bayanai a sarkar sama ta Google Cloud.
    5. Ana iya cire manhajar Flubot ta hanyar Safe Mode ko ta amfani da Manhajar F-Secure. Don haka idan an ga wani dan tsurkun manhajar da ba a amince da shi ba a waya, sai a nemi kwararru su kokarta.
    6. Idan ta gagara, mafi sauki a yi factory reset domin a rabu da barnar da manhajar Flubot din ka iya haifarwa
    7. A yi hanzarin tuntubar banki idan ana zaton ko an yi wa mutum kutse. Hakanan sauran akawuns na SM, a yi hanzarin canja kalaman sirri watau password.

    Muna rokon Allah kiyayewar sa daga dukkanin abin ki.

    Danladi Z. Haruna (ACA, ACS), ya rubuto daga Kano

    Turawa Abokai

    RUBUTA AMSA

    Rubuta ra'ayinka
    Rubuta Sunanka a nan