Ganduje baya cika alƙawari: Gargaɗin Mu’az Magaji ga Malam Ibrahim Shekarau

686

Tsohon Kwamishinan kula da ma’aikatar ayyuka da gidaje ta jihar Kano Mu’azu Magaji Dan Sarauniya, ya gargadi tsohon Gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau da kada ya kuskura ya karbi tayin sulhu da Gwamnan Kano Alhaji Abdullahi Umar Ganduje, domin a cewarsa Gandujen baya cika alkawari.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Mu’az Magaji a lokacin ana danyen ganye

Muazu Magaji ya wallafa a shafinsa na Facebook cewar, ko a baya Gwamna Ganduje ya yiwa Malam Ibrahim Shekarau alkawari amma bai cika masa, dan haka yake gargadinsa da kada ya kuskura ya karbi duk wani tayin sulhu da Gwamna domin ba mai cika alkawari bane.

Tuni dai rikici ya dabaibaye jam’iyyar APC reshen jihar Kano, biyo bayan zaben shugabannin jam`iyyar APC na jihar inda aka samu ɓangarori biyu da su ka gudanar da zabe a Kano, wato da tsagin gwamna Ganduje mai Abdullahi Abbas da kuma tsagin Sanata Malam Ibrahim Shekarau wanda ya yadda da shugabancin Ahmadu Haruna Zago.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan