Sallar Gani: Sarkin Gumel ya yabawa gwamnatin tarayya akan samar da tashar lantarki

509

Mai martaba Sarkin Gumel Alhaji Ahmed Muhammad Sani ya yabawa gwamnatin tarayya bisa samar da tashar lantarki a karamar hukumar Gagarawa da ke jihar Jigawa.

Mai martaba sarki ya yi yabon ne a wajen bikin sallar Gani ta bana, inda ya jaddada cikakken goyan bayan jama’arsa ga gwamnatin jiha da kuma gwamnatin tarayya.

Mai martaba Sarkin Gumel Alhaji Ahmed Mohammed Sani

Ya ce samar da tashar lantarki za ta taimaka wajen bunƙasa tattalin arzikin al’ummar masarautar Gumel da na jihar Jigawa.

Haka kuma Sarkin ya kuma yabawa gwamnatin jihar Jigawa bisa gudanar da aiyukan raya ƙasa a fadin masarautarsa.

Bikin sallar Gani na bana ya samu halartar mahaya dawaki da makada da maroka daga ciki da kuma wajen jihar Jigawa da ma kasashe makwabta.

Wani ɓangare na mahaya a bikin Sallar Gani ta bana a Gumel

Haka kuma bikin hawan sallar gani na daya daga cikin bukukuwan da masu sarauta da kuma dawaki ke kece raini a cikinsa.

A kan yi wa dawakai ado irin na alfarma da burgewa. Mutane da dama dai kan halarci wannan biki na hawan sallar gani domin kashe kwarkwatar idanunsu.

Bikin Sallar Gani a Masarautar Gumel

A ƙarshe mai martaba Sarkin Gumel Alhaji Ahmed Muhammad ya shawarci manoma da su hanzarta kwashe kayayyakin amfanin gonarsu da zarar sun kammala girbi da yanka domin wanzuwar zaman lafiya a tsakanin Fulani da manoman masarautarsa

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan