Sarkin Musulmin Najeriya, Mai Alfarma Sa’ad Abubakar III, ya girmama wani direban babur mai ƙafa uku mai suna Akilu Haruna Ahmad da kyautar dubu N500,000 sakamakon mayar wa da kuɗin tsintuwa da ya yi da suka kai N500,000 a Jos, babban birnin jihar Filato.
Mai Alfarma Sarkin Musulmin, a wani taro da aka yi a Babban Masallacin Jos, ya ce wannan direban babur ya nuna koyarwar addinin Musulunci.
Akilu, ɗan shekara 40, yana haya ne da babur ɗin mai ƙafa uku.
A ranar Alhamis, 14 ga Oktoba, 2021, ya tsinci wata jaka ƙunshe da wasu kayayyaki da kuma tsabar kuɗi har N500,000.
Bayan nan ne sai ya nemo mai jakar ya damƙa masa kuɗinsa.
Ko a 2017, Sarkin Musulmi ya ba wani direban babur mai ƙafa uku mai suna Bashir Usman kyauta wanda shi kuma ya mayar wa da wata fasinja mai suna Mama Ajimeh kuɗi har N582,400, ita ma dai a Jos.
Sarkin Musulmin, wanda ya samu wakilcin Sarkin Wase, Sambo Haruna, ya ce ya kamata mutane su yi watsi da halaye marasa kyau.
“Ya kamata mutane su san cewa idan mutum ya yi halin ƙwarai akwai lada. Muna alfahari da wannan saurayi wanda ya fito da kyawawan halayen Musulunci”, in ji shi.
Sarki Sambo, wanda shi ne Shugaban Jama’atu Nasril Islam, JNI, Reshen Jihar Filato, ya ce sai da Sarkin Musulmi ya umarce shi ya bincika ko mutumin ya tsinci kuɗin ya kuma dawo da su.
Ya ce bayan ya tabbatar da gaskiyar haka, sai Sarkin Musulmi ya aiko da N500,000 don a ba Akilu.
Shi ma Sarkin Kanam, Mai Martaba Muhammad Babangida Mua’zu, a lokacin da yake mika kuɗin ga Akilu ya ce abin da Akilun ya yi abin koyi ne ga dukkan Musulmi da ma wadanda ba Musulmi ba.