Ganduje Zai Ciyo Bashin Fiye Da Biliyan N20

282

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya aika da wasiƙa zuwa Majalisar Dokokin Jihar Kano don ta amince masa ya ciyo bashin naira biliyan N18.7 don rage raɗaɗin annobar COVID-19.

A ranar Talatar nan ne Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano, Hamisu Ibrahim Chidari ya karanta wasiƙar a zauren majalisar.

Wasiƙar ta ce Gwamnatin Jihar Kano tana neman sahalewar majalisar don ciyo wannan bashi, bashin da ta ce tuni jihohi da yawa suka karɓo bayan samun sahalewa daga majalisun dokokin jihohinsu.

Wasikar ta ce Gwamnatin Tarayya ta amince da bayar da rancen fiye da biliyan N18 ga jihohi 36 don rage raɗaɗin annobar COVID-19.

Gwamna Ganduje ya kuma aika da wata wasiƙar ga majalisar, inda yake neman sahalewarta don ciyo bashin fiye da biliyan N2 don siyo motocin nas-nas na BRT har guda 100.

Wasiƙar ta biyu ta ce Gwamnatin Jihar Kano ta biya miliyan N500 daga cikin kuɗin motocin na BRT.

Wasiƙar ta ce gwamnatin na son samun rancen ne don biyan cukon kuɗin motocin.

Bayan doguwar muhawara, majalisar ta amince da buƙatar Gwamna Ganduje ta ciyo bashin.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan