Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta lashi takobin cewa za ta share wa talakawa hawaye duk da matsin tattalin arziki da ake fuskanta a ƙasar.
Ministar Jin Ƙan Al’umma, Kare Afkuwar Annoba da Walwalar Jama’a, Sadiya Umar Farouq ce ta bayyana haka a yayin ƙaddamar da wani shiri mai suna Mobile Money Agents Training Programme ranar Litinin a Kano.
Ta ce haka ne ya sa ta ɓullo da Shirin Walwalar Jama’a na NSIP a matsayin wani mataki da za a rage wa marasa galihu raɗadin talauci.

Sadiya ta ce a shekaru biyar da suka gabata, fiye da iyalai miliyan 12 suka amfana da shirin na NSIP a faɗin ƙasar nan.
“Duba da sauyin rayuwa da waɗanda suka amfana da NSIP suka samu, Shugaba Buhari ya amince a ƙara wa’adin shirin don a tabbatar da cewa kowa an fitar da kowa daga talauci”, in ji ta.