Fitaccen ɗan bindigar nan mai suna Damina dake jihar Zamfara ya baƙunci lahira.
Damina, wanda yake da sansani a dajin Kuyanbana a yankin Ɗansadau dake yankin ƙaramar hukumar Maru, ya taɓa ƙona wata mata da ranta, kamar yadda rahotanni suka bayyana.
Damina ya mutu ne sakamakon faɗan da ɓangarensa ya yi da ɓangaren wani ɗan bindigar, Dogo Gide, a cewar jaridar Daily Trust.

Jaridar ta ce Damina ya sha kai munanan hare-hare da satar mutane da satar shanu a garuruwa da dama yankin Ɗansadau.
Damina ya mutu ne sakamakon raunukan da ya ji a fadan da aka yi a kusa da Chilin da Fammaje,wasu al’ummu biyu da ke ƙarƙashin ikonsa, a cewar rahoton Daily Trust da BBC Hausa ta rawaito.
Turawa Abokai