Hisba Ta Cafke Saurayin Da Ya So Ya Siyar Da Kansa A Kano

371

Hukumar Hisba ta Jihar Kano ta kama matashin nan ɗan shekara 26 wanda ya ce zai sayar da kan sa saboda talauci ya dame shi.


Hakan na ƙunshe ne a cikin wata hira da Kwamandan Hisba, Harun Ibn Sina ya yi da BBC Hausa.

A ƙarshen makon jiya ne hoton Aliyu Na Idris ya karaɗe shafukan sada zumunta ɗauke da kwali yana neman mai sayensa kan kuɗi naira miliyan 20, kamar yadda BBC Hausa ta rawaito.

Kwamandan Hisba ta Jihar Kano, Harun Ibn Sina

Kwamandan ya ce abin da Aliyu ya aikata haramun ne.

”E mun kama shi ranar Talata kuma ya kwana a hannunmu saboda abin da ya akaita haramun ne a addinin Musulinci, ba ka da damar sayar da kanka a kowanne hali ka tsinci kanka” in ji Ibn Sina.

Aliyu Idris wanda tela ne, ya ce yana cikin matsalar kuɗi, don haka ne ya yanke shawarar sanya farashin naira miliyan N20, sannan ya yi wa mutumin da ya yi alkawarin sayensa hidima da zuciya ɗaya.

Kafin kama shi, Aliyu ya faɗa wa ‘yan jarida a Kano cewa: ”Na yanke shawarar sayar da kaina ne saboda talauci, idan na samu mai saye na shirya bai wa iyayena naira miliyan 10, na biya naira miliyan N5 a matsayin haraji ga gwamnati, naira miliyan N2 ga duk wanda ya taimake ni na samu mai saye na, sai na ajiye sauran don amfanin yau da kullum.”

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan