Tsohon Minista, Abba Sayyadi Ruma Ya Rasu

463

Tsohon Ministan Aikin Gona da Bunƙasa Karkara, Abba Sayyadi Ruma ya rasu.


Ruma shi ne tsohon Ministan Aikin Gona da Bunƙasa Karkara a lokacin gwamnatin marigayi Umaru Musa Yar’Adua. Ya rasu yana da shekara 59.


Wata majiya mai kusanci da marigayin ce ta bayyana haka ranar Laraba.


Majiyar ta ce tsohon ministan ya rasu ne ranar Laraba da rana a wani asibiti a Landan.


An haifi Ruma ne ranar 13 ga Maris, 1962.


Ya taɓa riƙe muƙamin Shugaban Majalisar Gudanarwa ta Asusun Bunƙasa Aikin Gona mai hedikwata a Rome.

Marigayin ya yi digirin farko a tarihi a Jami’ar Usman Ɗanfodiyo, Sakkwato, digiri na biyu a International Affairs daga Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya, da kuma digiri na uku a International Relations daga Jami’ar Abuja.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan