Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya yi alƙawarin cewa zai fara biyan naira N30,000 ga malaman makaranta a matsayin mafi ƙarancin albashi.
Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da Maitaimakin Gwamnan Kan Kafafen Yaɗa Labarai, Isa Gusau ya fitar ranar Talata.
A yanzu haka wasu malaman a jihar Borno albashinsu bai gaza naira 11,000 ba sakamakon ayyukan malaman bogi, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

“Ɗaya daga cikin manyan matsalolin harkar ilimin firamare a Borno a yau ita ce kula da walwalar malamai. Abin takaici ne a ce har yanzu akwai masu karbar naira N13,000 ko 11,000 a matsayin albashi.
“Ina so na tabbatar da cewa duk da ƙalubalen da ake fama da shi na tattalin arziki, muna aiki don ganin cewa kowane malami da ya cancanta a Borno yana karbar naira N30,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi”, in ji Gwamna Zulum kamar yadda BBC Hausa ta rawaito.