Shugaban Hukumar KAROTA ta jihar Kano, Baffa Babba Dan’agundi, ya sanar da korar ɗaya daga jami’in hukumar mai suna RTA ll Jamilu Gambo.
Gambo ya dai rasa aikinsa ne sakamakon yadda ya nuna rashin kwarewarsa a ya yin da ya ke bakin aikinsa inda ya jawo asarar fashewar wata tayar babbar mota sakamakon hatsaniya da suka samu tsakanin sa da direban babbar motar.
Hatsaniyar dai ta afkune a kan titun zuwa Haɗeja, da ke Jihar Kano, tare da janyo hankalin sauran direbobin manyan motoci toshe titin don nuna jajantawa ga abokin sana’ar su.
Mai magana da yawun Hukumar ta KAROTA Nabulusi Abubakar Kofar Na’isa, a madadin shugaban ya bayyana cewa korar jami’in na zuwane bayan wani zaman gaggawa da Hukumar su tayi da kwamishinan ‘yan sandan Jihar Kano, tare da cimma wasu yar jejeniyar ladaftar ga korarren jami’in na KAROTA.

Ya ce Shugaban KAROTA ya yabawa shugabancin ƙungiyar direbobi reshen jihar Kano, bisa shiga tsakani yayin da abin ya afku tare da ceton ran jami’in daga rasa ransa tare kuma da yabawa hukunar ‘yan sanda bisa gudun mawar da suka bayar da bada tabbacin samar da adalci ga duk wanda aka samu baida lafi.
Haka kuma hukumar ta baiwa al’ummar da suka bi hanyar haƙuri wanda harta kai ga wannan lamari ya ritsa da su.
Inda kuma yace tuni hukumar ta miƙa jami’in zuwa hannun ‘yan sanda don faɗaɗa bincike tare da biyan asarar da ya jawowa direban.