Rashin Tsaro: Kiristoci Za Su Gabatar Da Addu’a Ta Musamman

312

A ranar Alhamis ɗin nan ne Ƙungiyar ‘Yan Majalisa Kiristoci za ta gudanar da addu’a ta musamman don samun sauƙin matsalar tsaro a faɗin Najeriya.

Shugaban Ƙungiyar, Emmanuel Bwacha, Sanatan PDP daga Jihar Taraba ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai ranar Laraba a Abuja.

Ya ce za a gudanar da addu’ar ne a farfajiyar Majalisar Dokoki ta Ƙasa.

Shugaban Ƙungiyar ‘Yan Majalisa Kiristoci, Emmanuel Bwatcha

Ya ce David Abioye, bishof kuma Shugaban the cocin Living Faith Church Worldwide, LFC, shi ne zai zama babban baƙo mai jawabi.

Ya ce haka ma Mataimakin Shugaban Najeriya, Yemi Osinbajo zai halarta.

Har lokacin da ya samu muƙamin Mataimakin Shugaban Ƙasa a 2015, Mista Osinbajo, wanda Farfesan Fannin Shari’a ne, Babban Malami ne a cocin ‘Redeemed Christian Church of God’ RCCG.

Bwacha ya ce taron da za a yi shi ba lokacin kalaci zai yi addu’o’i don samun sauƙin wasu daga cikin matsalolin da suke fuskantar ƙasar nan.

Ya ce taron bara an yi shi ne a manhajar ga-ni-ga-ka ta Zoom sakamakon annobar COVID-19.

“Tashin farashin kayan abinci ba ya ware ɗan jam’iyya kaza, ba ya ware ɗan yanki kaza kuma ba ya ware ɗan ƙabila kaza. Kai, ba ya ware ɗan shekara kaza.

“Abin da ya dame mu shi ne mu yi addu’a game da dukkan abubuwa”, in ji shi.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan