Shugabanci A Najeriya: Malamai lokaci ya yi

    405

    Ƴan uwa ku dubi girman al’amarin shugabanci. Rayukan al’lumma, lafiyarsu, hankulansu, dukiyarsu, nasabarsu, zaman lafiyarsu, jin dadi da walwalarsu duk su na kan shugaba a matsayin amana wacce Allah zai tambaye shi a kanta. Ba shakka kula da wannan amanar da kokarin sauke ta kamar yadda Allah ya ke so sai wanda ya san Allah, ya san girman amana kuma ya yarda da hisabi a lahira. In da za kai tambaya a rukunan al’umma su wane su ka fi sanin girman Allah da sanin nauyin amana ba shakka da yawa za a ce maka MALAMAI.

    Idan haka ne sai ka ce to me yasa a garuruwan Musulmi ba a fiya sha’awar baiwa malamai amanar shugabanci ba? Me ya sa mulki sai ‘yan boko jahilai marasa tsoron Allah, wasu ma tsawon rayuwarsu ba abinda su ka iya sai sata da cin amana? Me ya sa dole sai su alhali an ce Dimokuraɗiyya a ke yi?

    Dakta Ibrahim Siraj Adhama yana huɗuba a masallacin juma’a na Sasib da ke birnin Kano

    Idan a da ne wasu za su iya cewa ai malamai addini kawai su ka sani amma ba su iya boko ba. Yanzun ma haka ne? Ko kusa! Malamai ma yanzu sun iya boko fiye ma da waɗansu ‘yan bokon. A Kano akwai malamin da na sani ban da dimbin ilimin da Allah ya ba shi na Alqur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW), ya na da ilmin boko da gogewar da Wallahi ko Majalisar Dinkin Duniya ka ba shi zai riƙe ta kuma kowa zai tabbatar ya cancanta. Bayan wannan ya na da tsoron Allah daidai gwargwado da tsentseni ga asali da kyakkyawar tarbiyya. Irinsa kuma ba ɗaya ba ne a Kano kuma akwai ire-irensa da dama a wadannan jihohin namu na Arewa Musulmi. Me zai hana mu ba wa irinsu dama? Har yaushe Malamai za su cigaba da wulakanta a gaban jahilan ‘yan siyasa wadanda ba komai su ka fi su iyawa ba saboda ɗan wani mukami ko ɗan wani abin duniya da bai taka kara ya karya ba? Don me su ba za su riƙe ragamar ba?

    Da na kai matsayin yin fatawa da na yi fatawar da za ta wajabtawa Malamai fitowa takara kuma da na yi fatawa cewa dole ne a zaɓe su. A ganina sun fi wadannan mabarnatan ‘yan siyasar. A fahimtata taqawarsu ba za ta bar su su sace biliyoyin kuɗaɗen mutane ba alhali mutane su na mutuwa a asibitoci saboda ba magani. A fahimtata saninsu da muhimmancin ilimi ba zai barsu su bar makarantu su lalace ba ilimi ya durkushe su kuma su dau kuɗi su gina gadoji ba. A ganina ba za su danne hakkokin ‘yan fansho da ma’aikata ba domin sun san ba su da hujjar yin hakan a gaban Allah. Sun san cewa ɗani ɗaya na ƙasa da su ka kwata ba bisa hakki ba zai zamar musu babbar matsala a lahira saboda haka ba za su wawure filayen mutane ba bisa zalunci da son zuciya. A dunkule kuma sun karanci irin tausayi, adalci da dabarun mulki irin na Manzon Allah (SAW) da sauran manyan magabata. Wannan zai taimaka musu gane mafita a lokutan tsanani da kuma shimfida mulki na adalci fiye da yadda duk wani ɗan boko zai yi.

    Na sani cewa ‘yan siyasa sun lalata siyasa, sun gurɓata ta, sun kazantar da ita ta yadda duk wani mutum mai daraja ta gaskiya zai kyamace ta. Amma anya wannan ba dabara ce ta hana mutanen ka kirki su shiga a dama da su ba don a bar su su yi ta cin karensu ba babbaka?

    Lokaci ya yi da Malamai za su canja tunani su cire tsoro su yi abinda ya wajaba na kubutar da al’umma daga hannun azzaluman masu mulki. Ya wajaba Malamai su fito su gabatar da kansu ko mu mu fito da su; idan mafi yawan jama’a kuma su ka juya musu baya to wannan su ta shafa, su dai sun fita har a gaban Allah. Wannan fahimtata ce.

    Allah ya ba mu ikon gyarawa!

    Dakta Ibrahim Siraj Adhama malami a tsangayar sadarwa da harkokin aikin jarida da ke jami’ar Bayero da ke Kano.

    Turawa Abokai

    RUBUTA AMSA

    Rubuta ra'ayinka
    Rubuta Sunanka a nan