‘Yan Damfara sun Tilasta wa CBN Sauke Manhajar E-Naira Daga Play Store da App Store

460

Shagunan sayar da manhajojin salula sun sauke manhajar kuɗin intanet na e-Naira daga shafukansu kwana uku bayan shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da ita.

A safiyar Alhamis ne aka lura babu manhajar ta e-Naira a shagunan Play Store (masu Android) da kuma App Store (masu Apple).

Sai dai wa su da suka sauke manhajar tun farko sun ce, ta na aiki a wayoyinsu zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.

Lamarin na zuwa ne dai-dai lokacin da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya ankarar da ‘yan Najeriya game da ayyukan wa su “miyagu” da ke yunƙurin cutar mutane da sunan e-Naira.

Mutanen a cewar CBN, sun buɗe wa su shafukan sada zumunta da sunan babban bankin inda suke yaɗa cewa ya na raba kuɗin e-Naira har biliyan 50.

A ranar Litinin da ta gabata ne Shugaba Muhammadu Buhari, tare da Mataimakinsa Yemi Osinbajo suka ƙaddamar da kuɗin na e-Naira a Abuja, babban birnin ƙasar.

CBN ya ce, ya samar da kuɗin ne domin bai wa kowane rukuni na ‘yan Nijeriya damar gudanar da harkokin kuɗinsu cikin sauƙi bayan ya haramta amfani da sauran kuɗaɗen intanet na cryptocurrency.

Babban bankin na Najeriya ya faɗa cikin wata sanarwa ranar Laraba cewa “miyagun” na ƙoƙarin cutar ‘yan Najeriya ne waɗanda ba su ji ba su gani ba.

“CBN ya lura da ayyukan wa su miyagu da kuma wani shafin Twitter mai suna @enaira_cbdc da aka ce na CBN ne,” a cewar sanarwar.

“Shafin na bogi da kuma mutanen su na ta yaɗa saƙonnin da suka shafi e-Naira da zummar jawo hankalin ƴan Najeriya da cewa CBN na raba e-Naira biliyan 50.

‘Waɗannan miyagun sun dage sai sun zalunci mutane ta hanyar maƙala wani adireshi a jikin saƙonnin nasu suna rokon mutane su shiga domin samun kasonsu a biliyan 50 din.”

Tun farko CBN ya ce, an samar da e-Naira ne ta hanyar fasahar da ake kira Blockchain Technology da zummar ba ta tsaro ta yadda ba za a iya yin jabunta ba

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan