Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa cin bashin da gwamnatin jihar ta ke yi ƙarƙashin gwamna Abdullahi Umar Ganduje ba daidai bane
Sanata Rabi’u Kwankwaso ya bayyana hakan a jiya a cikin wata hirar da aka yi da shi a gidan Talabijin na Arise, inda ya nuna takaici kwarai da cin bashi da gwamnatin jihar Kano ta Dokta Abdullahi Umar Ganduje take yi.
“Ba daidai bane ka rika zarya kana ciwo bashi a gine-gine ko abubuwan da ba a bukatarsu a yanzu”
Haka kuma tsohon Gwamnan gwwmnan ya bayyana cewa bai taba ciyo bashi ba lokacin da ya yi gwamnan jihar na tsawon shekara takwas.
Kwankwaso ya soki Gwamnan Jihar Kano mai ci, Abdullahi Umar Ganduje, kan jefa jihar cikin kangin bashi, babu gaira, babu dalili.

A cewarsa, ana bin Kano bashin kudi da ya kai biliyan N187, abin da ya ce hakan babban kuskure ne a bari ya ci gaba da faruwa.
Kwankwaso wanda shi ne jagoran tafiyar siyasa ta Kwankwasiyya, ya ce dukkanin ayyukan da gwamnatin jihar ke yi a yanzu, ana aiwatar da su ne ta hanyar ciyo bashi, wanda kuma babu bukatar hakan.
“A Kwankwasiyya, ba mu yarda da ciyo bashi ba, sai dai idan cin bashin ya zama dole, don haka zan iya cewa tun daga 1999 zuwa 2003 ban taba ciyo bashi daga cikin gida ko kasashen ketare ba.
“Amma kuma sai da muka biya dukkannin bashin da gwamnatin dana gada ta ciyo.
“Sannan da na sake dawowa a 2011 mun sake samun tarin bashi, akwai bashin da muka tarar na Dala miliya 200 da aka ciyo daga Bankin Duniya, wanda ya shafi yaki da cutar maleriya,” inji shi.