Fitila: Sharhi Da Fashin Baƙin Manyan Rahotannin Makon Jiya

527

A wannan mako wannan fili zai fara duba ne akan wani gagarumin taro wanda cibiyar bunƙasa Fasahar Sadarwa da Cigaban Al’umma wacce aka fi sani da CITAD ta shirya a garin Kano.

Taron na bana wanda aka yi wa laƙabi da Alfanun Fasahar Sadarwa da Kafafen Sada Zumunta Wajen Kyautata Jagoranci na Kwarai ya tara mashahuran mutane tare da gabatar da kasidu fiye da 65.

Taron Citad

Wannan taro an shirya shi ne domin lalubu hanyoyin da za’ayi anfani da su a samar da ingantacciyar gwamnati tare da jagoranci a Najeiya.

Taron da aka fara a watan July na shekarar 2019 an ƙirƙiro shi ne domin gano yadda za’a iya anfani da kafafen sada zumunta na zamani tare da sauran kafafen sadarwa domin inganta rayuywar al’umma duba da ɗumbin tarin al’umma musamman matasa da suke anfani da shafukan a fadin duniya.

Sai dai wani hanzari ba gudu ba, a kasashe masu tasowa gwamnatoci sun daɗe suna ƙoƙarin hana al’umma cin alfanun waɗannan shafuka ta inda suke fakewa da wasu batu domin hana al’umma faɗin albarkacin bakinsu.

Manyan baƙi

Ko a wannan shekara, gwamnatin Najeriya ta dakatar da amfani da shafin Twitter saboda wasu zarge-zarge marasa tuse da take yiwa shafin.

Daga wani ɓangaren kuma, su kansu kafafen ana yi musu zargin wurin rura wutar kiyayya, gaba da kuma rigingimu a tsakanin mabanbantan ƙabilu, addinai da kuma yan siyasa.

A jawabin sa a wurin taron na wannan shekara, babban jami’i a Cibiyar Demokariyar da Cigaban Al’umma wato CDD, kuma tsohon shugban cibiyar, Farfesa Jibrin Ibrahim, ya koka matuƙa kan yadda kafafen ke bari ana amfani da shafukansu wajen rura wutar kiyayya a tsakanin ɓangararo a inda ya bayar da misali akan yadda wata tsohowar babbar jami’a a kafar sadarwa ta Facebook, Frances Haugen ta fitar da wasu bayanan sirru na yadda kafar ta Facebook ke bari ana anfani da ita wajen rura wutar gaba tsakanin ɓangarorin addinai, Siyasa da ƙabilanci.

Farfesa Jibrin Ibrahim

Wannan batu na sa yazo ne bayan da mai kula da harkokin na Facebook a yammacin Africa, Ebuka Ogbodo ya gudanar da ƙasidarsa mai taken “Yadda Facebook ke magance Labarun Karya da na Tayar da Tarzoma”.

A jawaban nasa yayi batutuwa masu yawa inda yayi bayanin yadda kafar tasu take kokarin ganin sun magance labarum karya da kalamai waɗanda ka iya haifar da tunzuri a cikin al’umma.

Haka ma shugabar Cibiyar Dimokaradiya da Cigaban Al’umma, Idayat Hassan wadda jami’i mai kula da laburan bogi a cibiyar ya wakilta wato Shamsudden Jibrin ta gabatar da mukala akan Labarun Bogi a Lokacin Annobar Korona.

Shugabar ta ce, laburan bogi sunyi matuƙar tasiri wurin yaɗuwar cutar, sannan sun sanya shakku cikin zukatan al’umma game da amincewa da sahihanci cutar. Haka zalika taron ya sami wakilcin Ministan Sadarwa wato Malam Isah Ali Pantami da Shugaban hukumar ƙirƙire-ƙirƙire (NITDA) ta kasa wato Kashifu Inuwa.

Sauran mashahuran mutane da suka gabatar da ƙasida da kuma waɗanda suka halarci taron sun haɗa da Dr. Chris Kwaja na Jami’ar Modibbo Adama University dake Yola, sai Professor Abdallah Uba Adamu tsohon shugaban Jami’ar NOUN wanda yayi jawabi game da masana’antar Kannywood, da Farfesa Attahiru Muhammad Jega, da Farfesa Habu Muhammad Fage, sai shugabar Amnesty International wato Osai Ojigbo, Farfesa Amina Kiadal ta Jami’ar Maiduguri. Haka zalika Mallam Ibrahim Tizhe, Chief (Eng.) C. O. Iromantu duk sun halacci taron.

A jawabinsa na maraba, babban Daraktan CITAD, Engineer Yunusa Zakari Ya’u ya ce babban maƙasudin shirya wannan taron shi ne a ɓullo da wasu hanyoyi da za’a iya amfani da su domin inganta harkokin mulki a wannan kasa tamu, sanna kuma dama cee ga masu halattar taron su koyi abubuwan da za’a tautauna musamman akan harkokin ƙirƙire-ƙirƙire waɗanda sune suke ciyar da ƙasashe gaba a yanzu, sai kuma yadda al’umma zasu haɗa kai domin kuɓutar da ƙasar daga matsalolin da suka dabaibaye ta.

Taron dai za’a a rinƙa shirya shi a duk shekara domin samarwa da al’umma musamman matasa wata kafa da zasu na tattaunawa akan matsalolin da suka shafe su dama kasa baki ɗaya sannan su samarwa da kansu mafita.

Engineer Yunusa Zakari Ya’u

Sai batu na biyo, a ranar Asabar ɗin da muka yi ban kwana da ita ne jam’iyar PDP ta gudunar da babban taron ta na ƙasa a birnin tarayya Abuja inda ta zabi shuwagabannin jam’iyar guda ashirin da daya (21).

An dai zabi senator Iyorchia Ayu a matsayin wanda zai jagoranci jam’iyar a zaɓen da za’yi mai zuwa bayan sulhu da yan takarkarin sukayi.

Sai dai ana gani cewa jam’iyar har yanzu tana cikin ruɗani duba da ɗumbin shara’o’in da suke gaban alƙalai game jam’iyar tare da mabanbantan ra’ayuyyuka kan wanda zai jagoranci jam’iyar a zaben mai zuwa.

Babbar matsalar ko ƙalubale dake dabaibaye da wannan jam’iya wanda masana ke ganin zai iya kawowa jam’iyar naƙasu a zaɓe mai zuwa shi ne game da fitar da ɗan takara.

In muka yi duba da masu zawarcin tikitin jam’iyar musamman daga jahohin Arewa kamar su tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, da tsohon gwamnan Kano Senator Rabi’u Kwankwaso, da gwamnan Sokkoto mai ci Aminu Waziri Tambuwal sai tsohon kakakin Majalisar Dattawa, Bukola Saraki zamu ga cewa lelle in ba an samu cimma matsaya ba tsakanin waɗannan yan takara ba, jam’iyar na iya faɗawa halin rikici wanda ka iya janyo rarrabuwar kai tsakanin yan jam’iyar.

Sai batu na gaba wanda shi ma abin lura ne game da wannan jam’iya, har yanzu dai waɗansu yan jam’iyar suna gaban kotu kan neman dakatar da taron da akayi a jiya asabar 30 ga watan July duk da dai kotun daukaka kara ta ba da izinin ayi taron to amma akwai yiyuwar su tafi kotun koli wanda in suka yi nasara ya mayarwa da jam’iyar hannun agogo baya.

Nan zamu jingine wannan batu zamu cigaba da bibiya domin sanin yadda zata ƙarke a kotu.

Filin Gyara Kayanka

Sai batun da zamu ƙarke da shi a wannan makon, zamu yi duba da yadda ake tafiyar da harkokin mulki ne a jihar Kano wacce ada ake yimata kirari da cibiyar kasuwanci ta ƙasashen yammacin Africa domin mu ga a halin da wannan jiha take ciki yanzu.

A hakikanin gaskiya wannan jiha ta shiga halin ni ƴasu, al’amura sun tababbare a jihar.

Kasuwancin da wannan jiha take alhari da shi ya fara dushashewa, sannan masu tafiyar da mulkin jihar hankalinsu ya koma kan wani abu daban.

Al’umma dai na kokawa kan yadda gwamnatin tafi mai da hankali kan yanka filaye a cikin hanyoyin kasuwannin jihar, da manya masallatai, da makarantu harma da maƙabartu wadda ke kawo ruɗani cikin al’umma.

Muna kira da babbar murya ga mahukunta suyi duba akan wannan batu.

Ali Sabo Dan Jarida Mai Sharhi Akan Al’amuran Yau Da Kullum.

Za a iya samunsa ta aliyuncee@gmail.com

Kuna iya bibiyarmu ta kafafen sada zumuntarmu a

Facebook

YouTube

Instagram

Telegram Ko kuma ku aiko mana da gyara ko shawara ta adireshinmu na email – Labarai24@yahoo.com

Ku shiga group dinmu don samun labaru kullum 👉 https://chat.whatsapp.com/EVy49win4h6KeRb6Uaxemg

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan