Gidauniyar Maryam Kofar Mata ta raba motoci da tallafi ga matasa fiye da 100 a Kano

566

Wata fitacciyar ƴar siyasa a jihar Kano da ke arewacin Najeriya, Hajiya Maryam Umar Kofar Mata ta raba tallafin kuɗi ga ƙungiyoyi da kuma ɗaiɗaikun mata fiye da guda ɗari (100) domin kama sana’o’in dogaro da kai.

Rabon tallafin da aka yi a ƙarƙashin gidauniyar Maryam Umar Kofar Mata wato Maryam Umar Kofar Mata Foundation, ya gudana ne a yau Lahadi, inda aka baiwa wasu daga cikin daraktocin gidauniyar ta Maryam Kofar Mata su biyar motoci domin saukaka musu zirga-zirga.

A lokacin rabon tallafin Hajiya Maryam Kofar Mata ta yi kira ga waɗanda su ka amfana da su yi ƙoƙari wajen ganin sun yi amfani da kuɗin yadda ya dace. Haka kuma ta buƙaci ƴan siyasa da su zama masu taimakawa na kasa da su a duk lokacin da su ka samu wata dama, domin hakan zai taimaka ƙwarai da gaske wajen rage talauci a cikin al’umma.

Hajia Maryam Umar Kofar Mata take jawabi a gurin rabon tallafin

Hakazalika, Maryam Kofar Mata ta bayyana cewa a dukkanin cikin masu neman kujerar gwamnan Kano a tutar jam’iyyar APC babu wanda ya fi dacewa kamar Alhaji Abdussalam Abdulkarim Zaura wanda aka fi sani da A.A Zaura.

Matashiyar ƴar siyasar wacce ta taɓa riƙe muƙamin shugabancin mata na jam’iyyar APC reshen jihar Kano, ta ce la’akari irin kyawawan manufofin da A.A Zaura ya ke da su ya sanya ita da jama’arta da ke faɗin jihar su ka ɗauki tafiyarsa.

Wannan rabon dai yana zuwa mako ɗaya da gidauniyar Maryam Kofar Mata din ta tabawa matasa guda ashirin (20) babura.

A karshe waɗanda su ka amfana da tallafin sun bayyana jin dadinsu tare da godiyar su ga Hajiya Maryam Umar Kofar Mata tare da ƙara nuna goyon bayansu a gareta.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan