Ƴan bindiga sun hallaka babban limamin masallacin Juma’a a Katsina

473

Wasu yan bindiga sun kashe Babban Limamin Masallacin Jumu’a na garin Sabon Garin Bilbis mai suna Liman Malam Adamu dake a karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina.

Kamar yadda muka samu, yan bindigar sun shiga garin na Sabon Garin Bilbis da kauyukan dake zagaye da shi a ranar Lahadi inda suka jima suna cin karen su ba babbaka.

Wani mazaunin garin mai suna Lawal Mamman Bilbis ya bayyana a wani rubutun da yayi a shafin sa na Facebook cewa “sun samu Marigayin ne a gonar sa tare da ma’aikata suna masa aiki suka ce zasu tafi dashi daji shi kuma yace musu su yi hakuri yana fama da matsalar ciwon kafa.

Lawal Mamman ya cigaba da cewa “daga nan sai ‘yan bindigar suka ce idan fa bai zo sun tafi ba kashe shi zasu yi a nan, shi kuwa yace sai dai su kashe shi idan ba zasu yi masa afuwa ba, nan take suka harbe shi ya amsa kiran Allah sannan suka tattare matan dake masa aikin suka tafi dasu daji.”

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan