Babu Wasu ‘Yan Ta’adda A Kano— NSCDC

331

Rundunar tsaro ta Nigeria Security and Civil Defence Corps, NSCDC, a Jihar Kano, ta ƙaryata labarin dake yawo a kafafen sada zumunta na zamani dake cewa ‘yan bindiga daga jihohin Zamfara da Katsina suna kwarorowa jihar Kano.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Jami’in Huɗɗa da Jama’a na NSCDC, DSC Ibrahim Idris Abdullahi ya fitar ranar Litinin a Kano.

Labarin da yake yawo a kafafen sada zumuntar ya ce ‘yan bindigar na kwarorowa jihar Kano sakamakon matsi da suke fuskanta daga jami’an tsaro.

A cewar labarin, ‘yan bindigar sun tare a ƙananan hukumomin Shanono, Gwarzo da Kabo, kuma a cewar labarin ‘yan bindigar sun fara haƙar ma’adinai.

“Mun gano cewa labarin ba gaskiya ba ne.

“Ranar 28 ga Oktoba, da misalin ƙarfe 9:00 na safe, an ga wasu mutane akan babura suna ficewa daga ƙauyen Danguzuri a ƙaramar hukumar Makarfi dake Jihar Kaduna. Suka bi ta Zarewa a Jihar Kano, suka biyo ta Hanyar Beli zuwa Babbarika, inda suka je ɗaurin aure a gidan wani mutum, Alhaji Shehu Danfulani.

“Bayan kammala ɗaurin auren, sai suka koma inda suka fito”, in ji DSC Ibrahim.

DSC Ibrahim ya ce jami’an tsaro sun yi wa Dagacin Zarewa da na Danfulani tambayoyi, kuma sun tabbatar musu da haka.

“Daga binciken da muka gudanar zuwa yanzu, ba wasu ‘yan ta’adda da suka tare a ƙananan hukumomin Gwarzo, Kabo da Shanono ko kuma dajin Dansoshiya”, in ji shi.

Sai dai ya ce NSCDC, bisa hadin kai da sauran hukumomin tsaron m, za ta ci gaba da sa ido don samar da cikakken tsaro.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan