Gini
Faɗuwar wani gini mai hawa 21 a jihar Legas ya yi sanadiyyar jikkata wasu mutane da dama.
Ginin da ba a kammala ginin sa ba yana unguwar Gerrard Road ne a Ikoyi.
Har yanzu ba a gano dalilin faduwar ginin da kuma mutanen da suka jikkata ba.
Tuni jami’an bada agajin gaggawa sun kai ɗauki a wajen wannan gini.
Dakta Olufemi Oke Osanyintolu, Shugaban Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Jihar Legas ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN, cewa tuni hukumar ta aika da ma’aikatanta wajen ganin yadda abin yake.
Turawa Abokai