Gwamnatin mulkin soja mafi lalacewa ta fi gwamnatin Buhari ta APC – Ortom

298

Gwamnan jihar Binuwai a yankin tsakiyar Najeriya Samuel Ortom, a ranar Litinin ya soki gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.

Gwamna Ortom ya ce gwamnatin mulkin soja mafi muni da aka taɓa yi a ƙasar nan ta fi gwamnatin APC mai mulkin ƙasar yanzu.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa gwamnan ya faɗi hakan ne a wani taron manema labarai jim kaɗan bayan komawarsa Binuwai ɗin daga taron jam’iyyar PDP da aka yi a Abuja.

Ya ce sakamakon taron jam’iyyar tasa ya nuna ƙarara cewa PDP ta shirya don karɓar mulkin ƙasar nan a 2023, yana mai zargin cewa wannan gwamnatin ta gaza a duk al’amuranta.

“Sun yi nasara wajen lalata tattalin arzikinmu da tsaronmu da harkokin rayuwarmu da ma duk wani abu da ya shafi ƙsar nan.

“Na karanta tarihin Najeriya da na waɗanda suka lalata mu ciki har da mulkin soji. Yawanci mukan ce gwamnatin farar hula mafi taɓarɓarewa ta fi gwamnatin mulkin soji.

“Amma a gaskiya gwamnatin mulkin soji mafi lalacewa ta fi gwamnatin APC da ke mulki a yanzu,” in ji Gwamna Ortom.

BBC Hausa

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan