Za a naɗa shugaban kamfanin jaridar Triumph Ɗan Masanin Tudun Wada

311

Mai girma Dankadan Rano, hakimin Tudun Wada Alhaji Muhammad D. Ibrahim zai naɗa shugaban kamfanin buga jaridu mallakin jihar Kano wato Triumph, Malam Sabo Lawal Ibrahim a matsayin sabon Dan Masanin Tudun Wada shekara biyu bayan rasuwar Malam Umar Sa’idu Tudun Dan Masanin Tudun Wada na farko.

Mutanen da za a naɗa sarauta a masarautar Tudun Wada

Hakimin na Tudun Wada zai naɗa Malam Sabo Lawal Ibrahim da sauran wasu fitattun mutane da su ka fito daga yankin a ranar Asabar 6 ga watan Nuwamba a fadarsa da ke yankin ƙaramar hukumar Tudun Wada da ke jihar Kano.

Wannan ne dai karo na biyu da za naɗa sarautar ta Dan Masani a Tudun Wada, inda marigayi Malam Umar Sa’idu Tudun Wada shi ne aka fara ba wa sarautar.

Wanene sabon Dan Masanin Tudun Wada?

Hakimin Tudun Wada Alhaji Muhammad D. Ibrahim ya bar sarautar ta Dan Masani a gidansu marigayi Malam Umar Sa’idu Tudun Wada, inda ta faɗa kan ɗan yayansa.

Malam Sabo Lawal Ibrahim ɗa ya ke a gurin marigayi Malam Umar Sa’idu Tudun. An haife shi a cikin garin Tudun, inda ya yi makarantar firamare a Tudun Wada da kuma sikandare a Kano, wato Government Arabic College Gwale.

Malam Sabo Lawal Ibrahim

Haka kuma ya halarci jami’ar Jos da ke jihar Plateau, inda ya karanci harshen turanci a matakin digiri, ya sake komawa jami’ar Bayero inda ya samu digiri na biyu akan harshen turanci.

Malam Sabo Lawal Ibrahim ya yi aikin koyawar a kwalejin kimiyya da fasaha da ke Kano wato Kano State Polytechnic, kafin daga bisani ya shiga aikin jarida inda ya fara da jaridar Leadership a matsayin edita. Haka kuma ya yi aiki da gidajen jaridu daban-daban

Gabanin naɗa shi a matsayin Dan Masani, Malam Sabo Lawal Ibrahim shi ne yake rike da shugabancin gidan jaridar Triumph da ke jihar Kano a karo na biyu.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan