Kamfanin Man Fetur na Najeriya, NNPC ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su daina siyan man fetur suna ɓoyewa domin kuwa kamfanin yana da isasshen mai da zai wadaci ‘yan ƙasa.
Jami’in Huɗɗa da Jama’a na NNPC, Garba Muhammad ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.
Sanarwar ta ce man da NNPC yake da shi zai isa amfani daga nan har zuwa shekara mai kamawa.

NNPC ya ce yana nan yana tattaunawa da masu ruwa da tsaki don ganin cewa man fetur bai yanke ba a dukkan faɗin Najeriya.
Turawa Abokai