Ra’ayi: Kwankwaso da Ƴan Kwankwasiyya

202

In da za ka bibiyi tarihin siyasar Kwankwaso za ka lura ɗan siyasa ne jajirtacce ba cima zaune ba. Shi tun a da bai yarda kawai wai wani mutum ne zai nuna shi ko ba shi takara ba. A sau da yawan lokaci ya fi son a kaɗa ƙuri’ar zaɓen fidda gwani, ya kuma lashe.

Haka ake son ɗan siyasa, kuma haka tsarin siyasa ya ke. Wato ka miƙe ka nuna ƙarfin “capacity” ɗin ka, ba wai ka tsaya sototo ba wai kawai sai wani ya nuna ka, sannan wai za kai takara ba. Ba haka tsarin siyasa ya ke, ita siyasa rigar ƴanci ce ba siyasa rigar bauta ba.

Sai dai duk da jajircewar Kwankwaso da hazaƙarsa a siyasa, sai aka samu akasin halayyar Kwankwaso ga ƴan kwankwasiyya. Da yawa-yawan ƴan kwankwasiyya musamman masu neman takara sai su ka ajiye rigar ƴanci suka sanya rigar bauta.

Eh! Ta bauta mana! Yo! A tsarin Kwankwasiyya fa ba ya halatta ɗan takara ya je ya siyi “form” ɗin takara ba a karan kansa, sai dai Madugu ya zaɓi wanda ya ga dama ya basu takara, a basu dama siyan “form” Kenan in ku biyu kuna son kujera ɗaya, to in Madugu ya zaɓi abokin karawarka to kai fa sai dai a yi ma jaje.

A tsarin siyasa kuwa ba ya yiwu a ce mutum ɗaya shi ne ke da “final say” wajen zaɓen ɗan takara, wanda su ke da “final say” mutane ne. Don su mutane su suka san ƴan takararsu kuma su za a jagoranta su ne da damar su zaɓe su, ba wai haka kawai, ka ji ana cewa “sai abin da Madugu ya ce” ba, ko kuma mu “makafi” ne ba. A’a kuna da ido a bar ku ku yi amfani da shi. Shi tsarin siyasa ba wani matum ɗaya da za a ce, shi ne mai wuƙar yanke hukunci shi kaɗai, sai dai tsarin “dictatorship”

Yanzu don Allah akwai wani mutum da zai ce wa Kwankwaso kar ya siyi form ɗin takarar shugaban ƙasa ko kuma ya ce ya janye takararsa ya bar wa wani, kamar Tambuwal ko Atiku kuma shi Kwankwason ya kula shi? Sai dai a haɗu a akwatin zaɓe!

Don haka yadda Kwankwaso ya zama ɗan siyasa da yawan ƴan Kwankwasiyya ba ƴan siyasa ba ne, ƴan a amshin Shata ne kawai, don ɗan siyasa ƴanci ya sani ba makauniyar biyayyar mutum ba.

Mukhtar Mudi Spikin ya rubuto daga Kano

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan